HARISAWA SUNYI BIKIN DIYAR ANNABI (S.A.W.W) A KATSINA
*HARISAWA SUNYI BUKIN MAULUDIN DIYAR ANNABI (S) A KATSINA.* Bin Yaqoub Katsina. Hurras na harkar Musulunci karkashin jagorancin Shaikh Zakzaky (H) yankin Azzahra (A.S) Zone Katsina da kewaye, sun gudanar da gagarumin Mauludin Sayyida Zahra (A.S) Wanda suka saba gabatarwa duk shekara. Taron dai an fara shi ne da safiyar yau Lahadi 21/2/2021 a filin samji cikin garin Katsina. Bayan bude taro da addu'a da karatun Alkur’ani gami da wake daga mawakan Harisawa, sai aka gudanar da addu’a ta musamman kan jagora Shaikh Zakzaky (H) tare da rokon Allah Ya gaggauta kwato shi daga hannun azzalumai. Wannan Mauludi dai an kayata shi ne da nau’oin bukukuwa kala-kala wanda aka soma tun ranar Asabar inda aka fara da wasan kwallon kafa, sannan gasar wake sai makala (Paper Presentation) wanda kwamitin Ilimi Na Harisawa ya jagoranta. Zuwa ranar lahadi nan kuma aka kammala da faretin ban girma ga Sayyida Zahra (A.S). A wannan Gasar dai da aka buga an samu Unit 6 sun halarta a karkashi...