Tuna Baya: SAI YAUSHE LAUYA BAYERO DARI ZAI TUBA YA DENA KARE KARYA!?

Tuna Baya: SAI YAUSHE LAUYA BAYERO DARI ZAI TUBA YA DENA KARE KARYA!? Ranar: 2-3 November, 1998 (13-14 Rajab, 1419H) KOMAWA DA SU SHAIKH ZAKZAKY KOTU A KARO NA GOMA: Ranar litini 2 ga Nuwambar 1998 ya kamata a cigaba da shari’ar su Shaikh Zakzaky tare da yan uwa uku; Alhaji Hamid Dallami, Malam Abubakar Almizan da Malam Shittu Muhammad wadanda gwamnatin Abacha ta kai kara tana zarginsu da laifin sun ce "Babu Hukuma Sai Ta Allah." amma sai ya zama ba a kai su kotun ba, ba a kuma yi zaman ba, sannan ba a fadi dalilin hakan ba. Washegari Talata, 3/11/1998 sai aka kai su Malam din kotu da misalin karfe 11 na safe, amma sai 12:30 na rana Alkali Adamu Kafaranti ya shigo kotun. Nan mai gabatar da kara a ranar, Lauya Bayero Dari ya mike yace su ba a shirye suke da su cigaba da gabatar da karar ba, saboda babbar lauyar Gwamnati, Ann Ishaku ta bukaci ita ce za ta gabatar da karar ba shi ba, kuma wai bata da lafiya. Bayero Dari yace, shi a matsayinsa na karamin lauya bai kamata ...