Posts

TAKAITACCEN TARIHIN SHAHEED ABU MAHDI AL'MUHANDIS

Image
An haifi Jamal Jafaar Mohammed Ali Āl Ebrahim wanda aka fi sani da alkunyarsa ta Abu Mahdi al-Muhandis a ranar 1 ga watan Yulin 1954 a gundumar Abu Al-Khaseeb na lardin Basra na ƙasar Iraƙi. Mahaifinsa dai ɗan asalin ƙasar Iraƙi ne, ita kuwa mahaifiyarsa an ce asalinta Ba’iraniya ce ‘yar ƙasar Iran. A nan ne yayi karatunsa na firamare da kuma na sakandare har zuwa jami’a inda ya gama karatunsa a fannin injiniya a shekarar 1977, inda a dai wannan shekarar ce ya shiga harkokin siyasa inda ya shiga ƙungiyar Dawa Party wacce take adawa da gwamnatin kama-karya ta Saddam Husain ta ƙasar Iraƙin. A shekarar 1979 ne ya gudu daga ƙasar Iraƙin zuwa ƙasar Iran bayan da gwamnatin Saddam ɗin ta haramta ayyukan jam’iyyar Dawa Party ɗin a duk faɗin ƙasar. An ce ya zauna ne a garin Ahwaz tare da sauran Iraƙawa ‘yan gwagwarmaya da suke cikin Iran inda suka ƙulla wani haɗin gwiwa tare da dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran wajen samun horo da kuma ƙwarewa na soji don faɗa da gwamnatin kama...
Leader of the Islamic Revolution Ayatollah Seyyed Ali Khamenei (center) pays a visit to the home of Lieutenant General Qassem Soleimani, the commander of the IRGC Quds Force, to express his condolences over his assassination in a US airstrike in the Iraqi capital, Baghdad. During the meeting on Friday, Ayatollah Khamenei expressed his condolences to Soleimani's family over the assassination. The Leader said Soleimani "had been faced with martyrdom several times but he feared no one and nothing" in the path of fulfilling his duties and fighting enemies. Ayatollah Khamenei added that Soleimani was martyred by the "most vicious individuals in the world," a clear reference to the White House tenants. The Leader wished patience for Soleimani's family and all Iranians and hailed the move by people who took to the streets in several cities across the country to express their anger and condolences over the assassination. Iranian demonstrators, in their hun...

JAWABIN AYATULLAH EL'SISTANI AKAN HARIN DABBANCI AMURICA DA TAKAIMA DAKARUN IRAN A IRAQ

Image
Ayatullah Sistani: Harin Dabbanci Ya Yi Sanadiyyar Shahadar Jan Gwarzon Da Ya Sami Nasara A Fada Da Daésh          ~Daga Ishaq Mohd Kibiya A wani bayani da ya fitar a yau jumaá, babban malamin addinin musulunci na kasar Iraki, Ayatullah Sistani ya mayar da martani akan shahadar Kasim Sulamani kwamandan rundunar Kudus, a sanadiyyar wani harin dabbanci akan kwamandojin da su ka sami nasara a fada da Daésh. Kafafen watsa labarun kasar Iraki, sun ambato babban malamin addini na kasar yana yin kira ga wadanda lamarin ya shafa da su yi aiki kafada da kafada da gwamnatin Iraki. An karanta bayanin na Ayatullah Sistani ne a yayin hudubar jumaá da aka karanta a birnin Karbala. Bayanin na ayatullahi Sistani ya ci gaba da cea: “ A cikin saoín da su ka gabata manyan abubuwa sun faru a cikin kasar Iraki wacce ta ke fama da rikice-rikice, take kuma cikin wani yanayi mai hatsari; wadannan laifukan sun hada da kai wa sojojin Iraki hari a garin Kaím, wanda ya yi sanadin sh...

SAKON JAGORA SAYYID KHAMNE'I DANGANE DA SHAHADAR JANAR QASIM SULAIMANI...

Image
Sakon Jagora Sayyid Khamne'i Dangane Da Shahadar Janar Qasim Sulaimani ........ Babban kwamandan musulunci kuma abin alfahari ya sami daukaka. A daren jiya, ruhin shahidai masu babadayin matsayi, sun yi maraba da tsarkakken ruhin Kasim Sulaimani. Bayan shekaru masu tsawo yana yin jihadi cikin tsarkin niyya da jarunta a cikin fagagen gwagwarmaya da shaidanu da ashararai na duniya, da kuma wasu shekarun masu tsawo na neman shahada akan tafarkin Allah, a karshe Sulaimani abin kauna, ya kai ga samun wannan matsayin na koli. Mafi tabewa a tsakanin mutane sun zubar da jininsa mai tsarki. Muna mika sakon taáziyya da kuma murna ta wannan shahadar mai girma zuwa ga wanzajjen Allah a doron kasa, wanda rayukanmu su ke a matsayin fansa a gare shi, da kuma ruhinsa, haka nan ga alúmmar Iran. Shi ( Kasim Sulaimani) yana a matsayin kyakkyawan misali ne na wanda ya sami cikakkiyar tarbiyyar musulunci a karkashin koyarwar Imam Khumai, kuma ya tafiyar da dukkanin rayuwarsa ne a fagen jihadi...

TA'AZIYYAYAR 'YAN'UWA ALMAJIRAN SHEIKH ZAKZAKY(H) GA SHEIKH DAHIRU USMAN BAUCHI NA RASUWAR MATAR SA

Image
Almajiran Shaikh Zakzaky sun je ta'aziyyar Matar Shaikh Dahiru Bauchi. Daga Auwal Isa Musa. 'Yan uwa Musulmi Almajiran Shaikh Ibraheem Alzakzaky na Jahar Bauchi,sun kai ta'aziyya ga Shehin Malamin Addinin Musuluncin nan na 6angaren Darikar Tijjaniyya a Najeriya, Shaikh Dahiru Usman Bauchi a yau Laraba,bisa rasuwar mai Dakinsa wadda ta rigamu gidan gaskiya a ranar Lahadin nan da ta gabata. Tawagar Masu ta'aziyyar dai tana a kalkashin jagorancin wakilin Shaikh Zakzaky na garin Bauchi,Shaikh Ahmad Yashi. A yayin da suke kar6ar ta'aziyyar a mamadin Shaikh Dahiru Usman Bauchi,yalan Mamaciyar,sun kar6i ta'aziyyara hannu bibbiyu sannan kuma sun nuna jin dadinsu da wannan ta'aziyya. Tun farko,da yake Jawabi a yayin ta'aziyyar,wakilin 'yan uwan na Bauchi Shaikh Ahmad Yashi ya bayyana wannan rashi a matsayin wani rashi mai daci,ba wai ga shi Shehin Malami Shaikh Dahiru Bauchi ko Iyalan mamaciyar ba, a'a har ma ga sauran Al'ummar Musulmi baki ...

TARON MANYAN MALAMAN HAUZA AKAN WAYE EL'ZAKZAKY?

Image
Taron manyan Malaman Hauza da Dalibai kan kira a saki Malam [H] a Tehran GAGARUMIN GANGAMIN MANYAN MALAMAN HAUZA DA DALIBAI NA YANKIN TEHRAN-IRAN _Karkashin kulawar Ayatullahi Aliy Akbar Rashad._ *Wan nan wani sako ne na Musamman da yafi shafar ‘yan’uwa almajiran Sayyid Zakzakiy (H)* Laraba: 5/Jimada Ula/1441 11/10/1398 Shamsiyya 1/1/2020. Miladiyya, Kamar yadda aka saba gabatar da Tarurruka, Gangami da sauran Zamammaki don kiran a saki Jagoran Harkar Musulunci na Najeriya Sayyid Ibrahim Zakzaky (H) a Jamhuriyyar Musulunci ta Iran, yau ma dimbin Malamai da Dalibai ne na yenkin Tehran, suka gabatar da Taro danagane da halin da Sayyid din yake ciki . Taron ya samu halartar _Sayyida Suhailat Ibrahim Zakzaky_ GABATARWA. Malami mai gabatarwa ya bayyana cewa, taron yana kunshe da Wata farkawa ta Malaman Hauza, don nuna cewa Sayyid Zakzakiy (H) bashi kadai ba ne; Maraji’ai, Malamai, da Daliban Hauza, suna tare da shi. kasantuwar da basu da masaniya dangane da...

AL'MAJIRAN SHEIKH ZAKZAKY 38 GWAMNATIN BUHARI TA KASHE ACIKIN SHEKARAR DATA GABATA 2019

Image
ALMAJIRAN SHAIKH ZAKZAKY 38 JAMI’AN TSARO SUKA KASHE A SHEKARAR 2019 Daga Saifullahi M. Kabir A yayin da shekarar Miladiyya ta 2019 ke karewa a yau Talata, muna tunawa da irin ta’addancin gwamnatin Buhari a kan ‘yan uwa Musulmi almajiran Shaikh Zakzaky (H), wanda ya sabbaba samun Shahidai akalla 38 a cikin wannan shekarar. A ranar 9/7/2019 ne ‘yan sanda suka bude wuta a kan masu muzaharar kira a saki Shaikh Ibraheem Zakzaky, inda suka kashe mutane biyu a kofar majalisar tarayyar Nijeriya a garin Abuja. ‘Yan uwan da suka kashe a wannan ranar sune Shahid Jafar Mika’il Lafiya da Shahid Mahmud Umar Suleja. Bayan kwana uku da wannan waki’ar a ranar 11/7/2019 kuma ‘yan sanda suka kuma budewa masu muzahar kira a saki Shaikh Zakzaky din a garin Kaduna, inda suka kashe ‘yan uwa Musulmi guda biyu; Shahid Ahmad Nasir da Shahid Abubakar Aliyu Badikko. Kwanaki biyar bayan hakan, a ranar Talata 16/7/2019 ‘yan sanda suka kuma aukawa masu muzaharar kira a saki Malam Zakzaky a Kaduna, inda su...