WACE IRIN ƁARNA CE SHEIKH ABDULJABBAR NASIRU KABARA YAKE YIMA SHI'ANCI?
hrtvnetwork.ng@gmail.com WACE IRIN ƁARNA CE SHEIKH ABDULJABBAR YAKE YI, A SHI'ANCI? Waye Sheikh Abduljabbar? Assheikh Abduljabbar Ibn Sheikh Nasiru Kabara malamin Addini ne,kuma ɗan ɗarikar ƙadiriyyah ne shi mai bin mazhabar Imam Malik. San'nan kuma har yau Sheikh Abduljabbar Sheikh Nasiru kabara baitaɓa Ayyana kansa ba a matsayin ɗan shi'a. Amma yabada gudumawar da irin Ustazu Hamza Lawal ɗari (idan akwaisu) basu bada ba. Domin a tarihin Hamza Lawal bai taɓa ɗauko wani mutum daga gidan Sunnah ba, idan nace gidan sunnah ina nufi Hamza bai taɓa ɗauko wani bawahabiye ko sufi, ya maida su 'yan shi'a ba. Ko ta hanyar wa'azin sa ko ta hanyar mu'a malar sa ko kuma ta hanyar kyakykyawar ɗabi'ar sa. (Idan yana da ita) Mutanen da Hamza Lawal ke tare dasu, dukkansu za'a iya cewa 'yan harkar musulinci ne, waɗanda ko wace irin tafiya zaka samu mutane iri uku ne, akwai waɗanda zakasamu suna yin harkar ne domin neman tsira ga Allah (s.w.t) ko nace kyakyky...