Posts

Sheikh Adamu Tsoho Jos Ya Cika Shekaru 60; Tarihin Sheikh Adamu Tsoho A Taƙaice !

Image
  Sheikh Adamu Tsoho Jos Ya Cika Shekaru 60 Tarihin Sheikh Adamu Tsoho A Taƙaice ! Sheikh Adum Tsoho Jos (Malamin Addinin Musulunci Yau 21-Feb-2021 yayi daidai da ranar zagayowar Haihuwar Sheikh Adamu Tsoho Jos, kuma an haifi Shaikh Adamu a garin Jos ta jihar Plateau, ranar Alhamis 27 ga Ramadan 1382H daidai da 21/2/1962. Yau kimanin shekaru 59 kenan.  Mahaifinsa sunansa Malam Muhammad Sani, amma an fi kiransa da Tsoho, kakansa kuma Malam Ahmad Kiffa, wanda yana daya daga cikin mutane 14 da aka kwaso su daga Bauchi a wancan lokacin aka kawo su Jos da nufin su raya garin na Jos. Kamar yadda mahaifin Shaikh din ya tabbatar min a wani hira da na taba yi da shi a kan tarihin kafa garin Jos a kwanakin baya. Mahaifiyar Shaikh Adamu Tsoho kuwa sunanta Hajiya Amina, ba a fi shekaru 11 ba da Allah Ya mata rasuwa. A yayin da su goma ne a wajen mahaifinsu, sai dai mahaifin nasu ya tabbatar min da cewa Shaikh Adamu Tsoho na daban ne a cikin 'ya'yan nasa ta fuskacin tsayuwa da addini da kum

Haihuwar Mai Albishi, Annabi Muhammad (S)

 Haihuwar Mai Albishir, Annabi Muhammadu (s) Daga Marigayi Muhd Awwal Bauchi Manzon Allah Muhammad bn Abdullah (s.a.w.a)  (A bisa ingantattun ruwayoyi), an haifi Manzon Allah (s) ne a ranar 17 ga watan Rabiul Awwal, ko da yake wasu ruwayoyin sun ce ran 12 ga wanann wata ne, a garin Makka, a shekarar da ake kira da Shekarar Giwaye. Dalilin da ya sa ake kiran wannan shekara da haka kuwa shi ne wani gwamnan Sarkin Abbasiniya ne mai suna Abrahata ya shigo Makka da runduna mai yawa bisa kan giwaye (bayan ya kame garin Yaman) da nufin rusa Dakin Ka'aba da sauya alkiblar mutane zuwa San'a (domin a wancan lokacin mutane sukan kawo ziyarar bauta a Ka'aba) inda da ma tuni ya gina wani guri don wannan ziyara. Amma daga baya lokacin da Abrahata ya iso Makka da wannan runduna ta sa, sai Allah Ya aiko da wasu irin tsuntsaye dauke da tsakuwoyi a bakunansu, inda suka rinka jefo wadannan tsakuwoyi a kan wadannan runduna, nan take suka kashe sojojin da giwayen. Ta haka ne Allah Ya yi magani

Muzaharorin Qudus: Dubun-dubata Suka Halarta A Katsina

Image
Muzaharorin Qudus: Dubunnai Suka Shiga A Katsina. @Daga A.I Musa Voice of Sheikh Kamar yadda duk duniya a juma'ar karshen watan Ramadhan na kowace shekara, Musulmin duniya kan gudanar da Muzaharorin nuna goyon bayansu ga Palasdinawa daga cin zarafin da Isra'ila ke yi ma su a kullum, bana ma, 'yan uwa Musulmi almajiran Shaikh Ibraheem Yaqoub Alzakzaky(H) na garin Katsina a tarayyar Nijeriya, sun bi sahun tagwarorinsu Musulmin na sauran Kasashe, wajen gudanar da jerin goyon bayan Palstinawan. Jerin gwanon Muzaharar wanda ya fara da misalin Karfe 9:00 daidai na safiyar Juma'ar nan 25 ga Ramadhan 1442H (7 ga Mayu, 2021) ya samu halartar dubun-dubatar al'ummar Musulmi. Muzaharar dai ta tashi daga Unguwar Madawaki inda kaitsaye da wuce zuwa Babban Masallacin Juma'a, ta kuma karkata ta bi ta Mobil, ta zagaya ta zo Sabon layi, inda aka tuke ta Tashar Gagare. A lokacin gudanar da Muzaharar, dinbin al'umma ne dauke da hotunan Palasdinawa da hot

YAKIN BADAR BABBAR NASARACE GA MUSULUNCI

Image
Yakin Badar Babbar Nasara Ce Da Ke Tabbatar Da Kafuwar Daular Musulunci, Inji Farfesa Danladi Daga Ammar M. Rajab Farfesa Abdullahi Danladi, Malami a Jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya ya bayyana cewa yakin Badar babbar nasara ce da ke tabbatar da cewa daular Musulunci ta kafu babu mai iya nuna mata dan yatsa. Farfesan ya bayyana hakan ne a yayin muhadara kan ranar Badar da ya gudana a jiya Alhamis 17 ga watan Ramadan 1442 a garin Zariya. Taron ya gudana ne a muhallin Fudiyya dake Babban Dodo Zariya. A kowacce rana cikin watan Ramadan, ana gudanar da Tafsirin Alkur’ani mai girma wanda Shaikh Abdulhameed Bello ke jagoranta, sai dai a jiyan an gudanar da muhadara ce kan ranar Badar wanda Farfesa Abdullahi Danladi ya gabatar da jawabi.  Farfesa Abdullahi Danladi ya kawo tarihin yakin Badar tiryan-triyan, harma ya nuna yadda tun daga yakin Badar da aka yi, aka samu fasahar amfani da ‘camouflage’ da dakarun sojoji suke amfani da shi a yau.  A wani bangare na jawabinsa, Farfesa Dan

SHAIKH YAƘUBU YAHAYA YA YI WA RAUNI KASHEDI.

Image
SHAIKH YAƘUBU YAHAYA YA YI WA RAUNI KASHEDI.  An buƙaci 'yan uwa da kada su sakar wa rauni fuska har su ɗauka cewa akwai abinda basu iyawa. Shaikh Yaƙub  Yahaya ya bayar da wannan shawarar alokacin da yake jawabi  alokacin da 'Yan lajnar islamiyyu suka kaimasa ziyarar shekara - shekara da suka saba kaimasa.  Malamin ya bayar da misali da lmam Khumaini alokacin da aka kafa daula aka rasa masu gyaran jiragen sama,  saboda ɓarnar da Amerikawa sukayi a ƙasar inda ya buƙacesu da suje su gyara jiragen zasu iya.  Da kuma misalin Fital castro na cuba wanda ya ɗauki ƙarfafa ilimi musamman na likitoci,  da injiya, a matsayin hanyar fitar da ƙasarsa daga cikin ƙunci da maysaloli. Malamin ya yi kira ga Malaman islamiyyu da suƙara zage damtse wirin ba 'ya 'yan 'yan uwa karatu sosai musamman akan Ƙur'ani da Tajwid,   sai Tauhid,  da Akhlaƙ.  Waɗannan sunada mahimmaci sosai ga al'umma.  Shaikh Yaƙub Yahaya ya bayyana haka ne alokacin da  Shugan Lajnar ta Islami

SHEIKH ZAKZAKY; Bayan kammala jami'a

Image
— Bayan Kammala Jami’a: Daga: Cibiyar Wallafa da Yaɗa Jawaban Shaikh Ibraheem Zakzaky (H).  Bayan kammala Jami’a, Shaikh Zakzaky ya cigaba da gabatar da gwagwarmayarsa na yunkurin tabbatar da addinin Musulunci. Tun a shekarar ta 1979 ta bayyana balo-balo cewa akwai wata da’awa da ke kira a komawa tsarin addinin Musulunci. Sai dai tana jami’a ce kawai a tsakanin daliban jami’a, amma a waje ba a san da ita ba. Ana wannan halin ne, kawai sai ga juyin-juya halin Musulunci na Iran a watan February 1979. Ga wani Malamin addinin Musulunci ya kira mutane zuwa ga komawa nizamin Musulunci, kuma ya fafata tsawon shekaru, har yau gashi ya juya kasar ya kori nizamin kafirci ya tabbatar da na Musulunci. Wannan ya karawa Shaikh Zakzaky da masu ra’ayinsa kwarin guiwa sosai, cewa lallai wannan abin da suke da’awarsa mai yiwuwa ne in har sun dake. Juyin Musulunci na Iran ya kuma ba da amsa ga masu ganin cewa ba zai yiwu addinin Musulunci ya dawo yai iko da mutane ba, a yayin da ga wani Malam

SHEKARARSA 70 A DUNIYA...A cikin wannan shekarun ya kwashe da yawansu cikin Ibtila'I na zalumcin azzalumai- Rahama Abdulmajid

Image
SHEKARARSA 70 A DUNIYA... A cikin wannan shekarun ya kwashe da yawansu cikin Ibtila'I na zalumcin azzalumai. 1 Shekara shida kenan da aka daure shi daga shi har matarsa  2 A cikin wannan shekarunsa Saba'in Gwamnatoci suka karar da 'ya'yansa. 3 A cikin wannan shekarun an kashe dubban mabiyansa maza da mata manya da yara har da na goye da suke asalin yan Najeriya masu hakkin tsaro da kare lafiya a wuyan gwamnati. 4 A cikin wadannan shekarun aka rushe duk wani waje da ya mallaka  5 a cikin wannan shekarun ne Kotu ta rika bayar da belinsa gwamnati na take umarnin kotu. 6 A cikin wannan shekarun duka bai kira mabiyansa da su dauki makami kamar yadda inyamurai ke dauka su kwana lafiya, yarbawa ke dauka su kwana lafiya, Fulani ke dauka su kwana lafiya.  7 Laifinsa daya shine ya zabi hanyar da ya ke ganin ita ce addininsa a kasar da kundin tsarin mulkinta  yace kowa na da 'yancin yin addini yadda yake so cikin walwala. DA INA DA DAMAR BAYAR DA AWARD HAKIKA ZAN B