DDALILIN DA YASA MUKA CE AKORI SHARI'AR DA AKE MA MALAM ZAKZAKY(H)

Abin da ya sa muka nemi a kori shari’ar da ake wa Malam [H] – Barista Ishak Adam Barista Ishaka Adam na cikin Lauyoyin da ke tsaya wa Shaikh Ibraheem Zakzaky a karar da gwamnatin Jihar Kaduna ta shigar da shi shekaru biyu da suka gabata. A cikin wannan hirar da suka yi da Aliyu Saleh, fitaccen Lauyan ya bayyana dalilansu na shigar da bukatar kotu ta yi watsi da shari’ar da ake yi wa Shaikh Zakzaky da maidakinsa Malama Zeenah. Sannan ya bayyana abin da suke fatan samu a hukuncin da kotun za ta yanke ranar Talata 29 ga Satumba mai zuwa. ALMIZAN: Masu karatu za su so sanin abin da ya sa Lauyoyin Shaikh Zakzaky suka shigar da kara suna neman kotu ta yi watsi da shari’ar da ake yi masa wacce aka kwashe sama da shekaru biyu ana yi? BARISTA ISHAKA ADAM: Sakamakon gwamnatin Jihar Kaduna ta shigar da su Malam Zakzaky kara tana tuhumar su da aikata wasu laifuffuka guda takwas tun a watan Yuni na 2018, wanda aka fara shiga kotu a ranar 5 ga wata, har ya zuwa yanzu fiye da shekaru biyu ke nan...