Posts

HALIN DA ƘASA TAKE CIKI. ANRUFEWA SARAKUNA BAKI NE- Sultan Sa'ad Abubakar.

Image
Halin da kasa ke ciki A Najeiya: ' An rufewa Sarakuna da Malaman Addini baki ' – Sarkin Musulmi Mai alfarma Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar, ya ce sarakuna da malaman addini da ya kamata su rika sanya ido kan shugabannin siyasa wajen suna yin abin da ya dace, an rufe musu baki. Sarkin Musulmi ya bayyana haka ne lokacin da yake jawabi a wajen taron Tattaunawa a Tsakanin Addinai kan Zaman Lafiya karo na Uku na bana da aka gudanar a Abuja. Taron ma taken “Tattaunawa a Tsakanin Addinai: Karfafa Al’adar Zaman Lafiya da Adalci da Sulhuntawa, Mai martaba Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II, ya wakilce shi a taron. Ya ce: “Duk wanda ya kashe wani Kirista ko Musulmi mai aikata babban laifi ne kuma a haka ya kamata a dauke shi. Duk abin da nake ji a yau mamaya ce. Sarakuna da shugabannin addini da ya kamata su  sanya ido kan shugabannin siyasa don su aikata daidai ga jama’a,  an tilasta su yin shiru. I...

SALLACEWAR SOYAYYA BAYAN AURE.da yanda za a magance ta.

Image
*An bayyana Sallacewar dandanon Soyayya bayan Aure da rashin aza tubalinta tun farko saboda Allah.* Daga *_Auwal Isa Musa._* Malama Hadiza Wowo ta bayyana haka a lokacin da take gabatar da Lakca ga Ma'aurata,a wata Walimar Aure a ranar Alhamis din nan a Katsina. Malamar ta ce,zamantakewar auren nan da ake yi tana da Ka'idoji da Sharudda da Allah ya gindaya kuma muke da abubuwan koyi a zamantakewar daga Fiyayyen Halitta Manzon tsira(S) wanda shi ne makura a wajen kowace irin kyakkyawar dabi'a,wadda har Allah ya lazimta mana koyi da shi a cikin dabi'un,amma abin takaici yau an wayi gari masu shirin yin Aure har ma da yawa daga wadanda suka yi auren, ba su da masaniyar wadannan ka'idoji ko kuma sun yi watsi da su suna aikata son zuciyarsu. A wani bangare na jawabinta,Malamar,ta kuma Kalubalanci Masoyan da Soyayyarsu.                                                ...

HALIN DA IS'RAILA DA YAHUDAWA SUKE CIKI TUN BAYAN HARIN SOJIN IRAN A SANSANIN AMURIKA A IRAQ

Image
Nasir Isa Ali. -Halin da Israila da Yahudawa ke ciki tun bayan kashe Janar Qassim Sulaimani. -- Rahotanni sun tabbatar da cewar,manyan jami'an gwamnatin Isaraila sun shiga wasan buya,tare da yin kaffa-Kaffa wajen yin tafiye tafiye da yawan bayyana wajen taro tun bayan harin da Iran ta kai kan sansanonin sojan Amurka dake cikin kasar Iraqi. Domin hakan ya nuna cewar,Iran din zata hararsu a ko'ina cikin yankin Asiya. Daya daga cikin hujjojin dake tabbatar da hakan shine, kafin kai harin na Iran kan Amurka,an shirya cewar Ministan harkokin kasashen waje na H.K.Israila, Mr.Yisrael Katz zai ziyarci birnin Dubai dake UAE domin halartar wani taron baje koli a tsakiyar wannan watan na Junairu,amma sai aka janye ziyarar,kuma babu wani dalili kan janyewar. Amma jami'an ma'aikatar tasa ta harkokin waje sun sanar da cewar,an yi hakan ne bisa wasu manyan dalilai na tsaro. - Tun dai bayyanar wani rahoton sirri dake nuna cewar,shugaba Trump yayi amfani ne da wani rahoton sirri ...

AL'ƘALAMI KAFI REZA KAIFI. TARE DA M.I GAMAWA-Janar ƙasim suleimani: Amurika ta hadiyi tabarya.

Image
*ALKALMI KA FI REZA KAIFI* TARE DA M. I. GAMAWA *Janar Qaseem Soleimani: Amurka ta hadiyi ta barya!* Wata mas'ala da marubuci ke fama da ita a kullum, musamman rubutu a kan abin da ke gudana a yau da kullum shi ne rashin tabbas kan abin da zai rubuta. Fakam da yawa mai rubutu na iya kimtsawa tsaf don rubutu a kan wani abu, amma sai sawun giwa ya taka kafar rakumi. Na shirya don maida wa wani kumurcin Farfesa da ke amsa sunan Malamin tarihi a Nijar martani kan jahilcin da ya nuna game da tarihin Shehu  Dan Fodiyo, Hasken zamani, amma sai sawun giwa ya take na rakumi. Mun taka birki don magana a kan Qaseem Soleimani, wanda Amurka ta kashe a satin da ya gabata. Soleimani ya tafi kasar Irak a matsayin dan sakon kasarsa Iran bisa gayyatar da ita kanta kasar Irak ta yi masa. Ashe tafiyar ita ce ta karshe. Abin da ya samu wannan gwarzo shi ne abin da yake nema tuntuntuni. Abin nema ita ce SHAHADA. Yanzu Allah ya yi wa Janar Sulaimani gyadar dogo da abin da ya fi so fiye da k...

FACEBOOK YACE ZAI ƘULLE DUK WANI ACCOUNT DA YA ƘARA YIN RAFOTO AKAN GEN QASIM SULEIMANI

Image
Facebook Ya Haramta Saka Duk Wani Abu Da Ya Shafi Kasim Sulaimani Muma Abinda yasa bamu sanya fotonsa ba don kada su share. Janairu 12, 2020 - 1:05 PM Kamfanin sadrwa na facebook ya bada sanarwan daga yanzu zai rika cire duk wasu abubuwa da aka dora a kan shafinta danganci Kasim Sulaimni. Taskar watsa labarai ta Ahlul-Baiti-ABNA24- ta rawaito a cikin wata sanarwa da kamfanin facebook ya fitar a jiya, ya ce daga yanzu zai rika cire duk wani abu da aka dora a kan shafinta ya shafin Janar shaheed kwamandan sojojin Iran da Amurka ta kashe mako goda day a gabata da kuma duk wani abu da ya shafi dakarun kare juyin juya hali na kasar Iran. Bayanin ya ce kamfanin zai yi aiki 100% da dokar ta kasar Amurka wacce ta haramta duk wasu aikace-aikace da suka shafi dakarun kare juyin juya hali a kasar Iran, kuma zai share duk wani shafi da aka saka wani abu makamancin hakan. Tun daga lokacinda Amurka ta kashe shaheed sulaimani a makon da ya gabata ya zuwa yanzu, facebook ya share shafuffuka n...

KUKALLI JAWABIN C.I.A DAGA AMERIKA KUJI GASKIYAN DALIN DAYA YASA SUKA KA...

Image

EL-RUFA'I ƊAN TA'ADDA NE.

Image
WATA SABUWA: 'Elrufa'i kai ne ka yi wa Mutanen Jihar Kaduna Laifi,ba Shaikh Zakzaky ba' -Mabiya Alzakzaky. "A tsawon shekaru 40 cur na da'awarsa, Shaikh Ibraheem Zakzaky bai ta6a afkawa wani ba, kai ko cin bashin wani ya ki biya bai ta6a yi ba! Wani bai ta6a kai shi kara wajen yan sanda akan ya cuce shi ko ya take hakkinsa ba. Magoya bayansa ba su taba kwashe kayan wani ko su zubar masa a yayin taron su ba, bare su je su dira kan wani ko su kashe shi. Ba a taba yi ba! Kai kuwa Elrufa'i, sakataren gwamnatinka, ya fada karara cewa bayan da sojoji suka dira a kan Shaikh Ibraheem Zakzaky, inda suka kai kansu gidansa cikin dare, suka rika bude wuta, suka kwana biyu suna harbin almajiransa har sai da suka kashe daruruwan al'ummar Nijeriya, kai ne ka ba da umurni tare da wakilta wasu daga gwamnatinka, suka je suka taya sojoji haqin rami tare da bizne bayin Allah, al'ummar Nijeriya, mafi yawa 'yan jihar Kaduna, kuma Musulmi, su kimanin 347 a ramin bai-d...