Posts

Shaikh Yakubu Yahaya Katsina Ya Cika Shekaru 66: Yadda Aka Gudanar Da Taron Ranar Zagayowar Haihuwarsa A Bana.

Image
Daga Auwal Isa Musa. A ranar Lahadin wannan Makon ne 16 ga Rajab, 1442 H (1 ga Maris, 2021 M) Iyalan Shaikh Yakubu Yahaya hadin guiwa da wani Kwamiti na shirya taron ranar haihuwarsa, suka shirya taron zagayoran ranar haihuwar Malamin, Malamin wanda yake cika shekaru 66 cif duniya. Taron wanda farko ya soma gudana a zangon farko da misalin karfe 4:00 na Yammacin ranar da kuma zango na biyu wanda shi kuma ya gudana da misalin karfe 8:00 daren ranar (Majalisin Mawaka), ya samu halartar dimbin jama'a na ciki da na wajen Da'irar ta Katsina har ma da sassa daban-daban na wasu Da'irorin Kasar nan. 'Yan uwa na jini da na Addini (a cikin harka da wajen ta), Abokai, Makwafta, Abokan arzuka na Shehin Malamin duk sun halarci taron, inda wasu daga cikinsu suka gabatar da jawabai a taron dangane da tarayyarsu da Shehin Malamin tun tale-talen shekaru masu yawa da suka gabata a baya. Malam Husaini, abokin Malamin ne tun na Kuruciya, ya kuma gabatar da jawabi a kan jajircewar Malamin w...

"Duk Wanda Ya Yada Hoton Mace Babu Hijabi Yana Da Kamasho A Cikin Zunubin Da Ta Aikata..." - Shaikh Adamu Tsoho Jos

Image
"A 'yan tsakanin nan mun ga mutane ciki har da wasu 'yan uwa masu ta'ammuli da shafukan sada zumunta suna ta yada hotunan wata da aka ce 'yar wasar Hausa ce ba tare da Hijabi a jikinta ba. Yin hakan ko da kuwa da sunan yabo ne, kuskure ne. Ya kamata a yi yabo ne da abin da Allah ya halatta. Ana iya ambaton suna, ba sai an yada hotuna marasa Hijabi ba. Bai kamata a samu 'yan uwa cikin hakan ba.  Ya kamata Muminai su sani cewa duk wanda ya yada hoton Mace ba tare da Hijabi ba, yana da kamasho a cikin zunubin da ta aikata na rashin cika umurnin Allah (T) kan suturce jikinta. Domin ita Mace dukkan jikinta al'aura ne in ban da fuska da tafukan hannu. Kuma an wajabta mata boye ado da sanya Hijabi daga dukkan ajnabanta. Abin takaici ne yadda muke ganin har wasu 'yan uwa su kan turo hotunan iyaye ko 'yan uwansu Amawa babu Hijabi. Da ma yadda ya zama wasu 'yan uwa din, musamman matasa Mata, suna daukan hotuna tare da ado suna yadawa a kafafen sada zumunt...

KUNDIN HOTUNAN BIKIN BIRTHDAY NA SHEIKH YAQUB YAHAYA KATSINA (@66) 1442/2021

Image
Hotunan Bikin Birthday na sheikh Yaqub Yahya na shekarar ta 1442/2021

AYYUKAN NISFU RAJAB

Image
_______________يوم النصف من رجب________________ AYYUKAN YININ 15 GA RAJAB (YAU ASABAR) Yau Asabar ne 15 ga watan Rajab mai girma a kasar Nijeriya. Wannan ranar ne tsakiyar Rajab (Nisfu Rajab) rana mai falala da girma. Akwai ayyuka da aka ruwaito ana yi a wannan yinin, daga cikinsu akwai: 1- An so a yi wanka a wannan ranar na 15 ga watan Rajab Mai Girma. 2- An so a ziyarci Imam Husaini (AS); An samu ruwaya a kan hakan; An tambayi Imam Ridha (AS) cewa; A wace wata  ne zamu ziyarci Imam Husaini (AS)? Sai Imam (AS) yace: “A cikin Nisfu (rabin) Rajab da Nisfu Sha’aban.” 3- Sallah raka’o’i hudu (4); An ruwaito daga Abi Abdullahi (AS) yace; Adiyyu bin Thabit al-Ansary ya shiga wajen Imam Ali (AS) a ranar 15 ga watan Rajab (Nisfu Rajab), Sai ya same Shi (AS) yana sallah……… Bayan ya sallame sai ya daga hannayensa sama, sannan ya karanta wannan addu’ar ta kasa: " أللهم يا مذل كل جبار ويا معز المؤمنين، أنت كهفي حين تعييني المذاهب وأنت بارئ خلقي رحمة بي، وقد كنت عن خلقي غنياً، ولولا رحمتك لكن...

Yunƙurin Hana Al'majirci; Ga abinda Sheikh yaqub Yahaya yace...

Image
Kokarin Hana Bara Da Almajiranci: Sakon Sheikh Yakubu Yahaya Ga Gwamnati Sheikh Yaqub Yahaya Daga: Bilya Hamza Dass Sheikh Yakubu Yahaya, sananne Malamin Addinin Islama ne mazaunin garin Katsina, me karantarwa tsawon shekaru, kuma yana daga cikin Almajiran Sheik Ibraheem Zakzaky. Malamin ya aika sako ga hukumomi da Gwamnatoti a kokarin da suke na hana tsarin karantarwa na Almajiranci da Bara, inda ya bayyana ra'ayin shi da kuma yanda yake kallon yakamata ayi, yayi Jawabin ne a wata ganawa da yayi da manema labarai a jihar kwanakin baya. “To abinda muke kallon wannan shine mukaddima na rufe makarantun Allon duk kasar nan baki daya. Domin yanzu abinda gwamnati ke babatu akan shi shine makarantun allo sun dame su da bara basuson bara. Bamuce bara addini ne ya kawota ba, bamuce bara dede ne ba, yin bara ba ba dede bane, amma menene ya sanya musulmi suka zama mabarata? ai da can kasar a hannun su take gidan Mallam ake biyawa aci abinci har a dauka akai gida, da bature yazo y...

MAULUDIN IMAM ALI (A.S) A GARIN ZARIYA

Image
MAULUDIN IMAM ALI YA KAYATAR AGRIN ZARIA wajen yanka Al'kakin Birthday Imam Ali  Alhamis 13 ga watan rajab     Wanda yazo daidai da 25 ga February inda aka gudanar da mauludin imam Ali bin abi dalib data gudna a muhalin fudiyya zaria. Anfara maulud din da misalin karfe hudu na yamma inda aka fara da bude taro da addua,kana daga  bisani aka gabatar da display. yan uwa sha'irai ma ba'a barsu bayaba inda sukaita rere baitocin na yabon  Imam Ali. Malam Aminu sakatare shine yazamo bako mai jawabi na farko malamin yayi bayanai masu gamsarwa dangane da janibin imam Ali. Cikin jawabin nasa malamin yanacewa " Imam Ali shine mutun na farko kum shine na karshe da'aka haifa a dakin qa'aba" haka zalika ya cigaba da cewa Imam Ali yayi sharia baa canzata har  a wajen Allah S.W.T Bayan ya kammala ak gabatar da mai jawabi na gaba malam Ibrahim usman na malam Tijjani khalifa zaria. Malamin yafara ne da bada tarihin  imam Ali inda yakecewa " kamar yadda ...

MAULUDIN IMAM ALI A MARKAZIN 'YAN'UWA NA KATSINA @2021

Image
MAULUDIN IMAM ALI (A.S) YA CI GABA A MARKAZ KATSINA. Sheikh Yaqub Yahaya Katsina Daga Bin Yaqub Katsina Yanzu haka Shaikh Yakubu Yahya Katsina na ci gaba da jawabin Mauludin Imam Ali (A.S) da yammacin nan na ranar Alhamis 13,rajab1442 dai dai da 25/2/2021. Bayan mawaka sun gama wakokin yabon Imam Ali (A.S) sai Shaikh Yakubu Yahya Katsina ya ci gaba da jawabinsa. Da farko dai Shaikh ya gode ma Allah bisa wannan babbar ni’ima da Allah yayi ma al’umma da duniya baki daya. Har wa yau Shaikh din ya dora karatunsa na yau ne a kan Kore shubuhar da aka rudi al’ummar Musulmi da ita na cewa; Baban Imam Amirul Mumineen (Ali) ba musulmi ya rasu ba, wato Sayyid Abu dalib. Shaikh ya ci gaba da karyata wannan shaci fadin zance inda yake cewa “Manzon Allah (S) shi ne ya sallaci Abu dalib kuma shi ne mutumin farko da ya fara shaidawa da Annabtar Annabi tun Annabi na karami, (a wajansa)”. Hotunan taron ne muka dauko maku da ke gudana a Sabuwar Markaz Katsina. ...