TARIHIN SHEIKH ZAKZAKY DAGA BAKIN SA 2

TARIHIN SHAIKH IBRAHEEM ZAKZAKY DAGA BAKINSA (2) — Daga Littafin HARKAR MUSULUNCI Na Cibiyar Wallafa Cigaba.... A lokacin da nake jami’a akwai wani yanayi da na samu, wanda kuma shi ya taimaka wajen canza rayuwata. Lokacin da na shiga (jami’a) kamar kowane dalibi, fatata shine na kammala jami’a wala’alla na je na kama aiki, ko kuma ma na cigaba da karatu a nan jami’a din, to amma yanayin da muka samu kanmu a ciki a wannan lokacin na karshen 70s, kamar za a iya cewa akwai musayar ra’ayi dangane da abin da ya dace ya zama makomar kasa. Lokacin kwaminisanci na tashe sosai, kuma da yawan dalibai da suke nuna sun waye, Kwaminisanci suke yi. Haka suma cikin Lakcarori wadanda suke nuna su cigababbu ne to Kwaminisanci suke. Saboda haka Kwaminisanci kamar shine wata alama ta cigaba. Kuma Kwaminisanci na da matsalar cewa suna ganin addini kamar wani mummunan abu ne. Kuma su kan ta yin hujumi a kan addini baki daya, da kuma musamman ma Muslunci. Suna ta sukan Musulunci, suna nuna kamar ...