AYYUKAN NISFU RAJAB

_______________يوم النصف من رجب________________ AYYUKAN YININ 15 GA RAJAB (YAU ASABAR) Yau Asabar ne 15 ga watan Rajab mai girma a kasar Nijeriya. Wannan ranar ne tsakiyar Rajab (Nisfu Rajab) rana mai falala da girma. Akwai ayyuka da aka ruwaito ana yi a wannan yinin, daga cikinsu akwai: 1- An so a yi wanka a wannan ranar na 15 ga watan Rajab Mai Girma. 2- An so a ziyarci Imam Husaini (AS); An samu ruwaya a kan hakan; An tambayi Imam Ridha (AS) cewa; A wace wata ne zamu ziyarci Imam Husaini (AS)? Sai Imam (AS) yace: “A cikin Nisfu (rabin) Rajab da Nisfu Sha’aban.” 3- Sallah raka’o’i hudu (4); An ruwaito daga Abi Abdullahi (AS) yace; Adiyyu bin Thabit al-Ansary ya shiga wajen Imam Ali (AS) a ranar 15 ga watan Rajab (Nisfu Rajab), Sai ya same Shi (AS) yana sallah……… Bayan ya sallame sai ya daga hannayensa sama, sannan ya karanta wannan addu’ar ta kasa: " أللهم يا مذل كل جبار ويا معز المؤمنين، أنت كهفي حين تعييني المذاهب وأنت بارئ خلقي رحمة بي، وقد كنت عن خلقي غنياً، ولولا رحمتك لكن...