Posts

Տᕼᗴᛕᕼ ᗪᖇ ᎥᗷᖇᗩᕼᎥᗰ 乙ᗩᛕ乙ᗩᛕƳ

Image
 𝘼𝙣𝙚𝙢𝙞 𝙩𝙨𝙖𝙧𝙞𝙣 𝘼𝙡𝙡𝙖𝙝 𝙙𝙖𝙜𝙖 𝙉𝙖𝙝𝙞𝙨𝙖𝙧 𝙬𝙖𝙩𝙖𝙣 𝙨𝙖𝙛𝙖𝙧. —𝘾𝙚𝙬𝙖𝙧 𝙅𝙖𝙜𝙤𝙧𝙖 𝙎𝙝𝙚𝙞𝙠𝙝 𝘿𝙧 𝙄𝙗𝙧𝙖𝙝𝙞𝙢 𝙕𝙖𝙠𝙯𝙖𝙠𝙮.(𝙃)  ᗷᎥՏᗰᎥᒪᒪᗩᕼᎥᖇ ᖇᗩᕼᗩᗰᗩᑎᎥᖇᖇᗩᕼᎥᗰ. Watan Safar, wata ne mai yawan nahisa. Masibobi na yawan sauka a watan Safar, saboda haka maganin masibobi addu'a da sadaka. Saboda haka a kiyaye da yin addu'a, musamman addu'ar: يَا شَدِيْدَ الْقُوٰى وَ يَا شَدِيْدَ الْمِحَالِ يَا عَزِيْزُ يَا عَزِيْزُ يَا عَزِيْزُ ذَلَّتْ بِعَظَمَتِكَ جَمِيْعُ خَلْقِكَ فَاكْفِنِيْ شَرَّ خَلْقِكَ يَا مُحْسِنُ يَا مُجْمِلُ يَا مُنْعِمُ يَا مُفْضِلُ يَا لَاۤ اِلٰهَ اِلَّاۤ اَنْتَ سُبْحَانَكَ اِنِّيْۤ كُنْتُ مِنَ الظَّالِمِيْنَ فَاسْتَجَبْنَا لَهُ وَ نَجَّيْنَاهُ مِنَ الْغَمِّ وَ كَذٰلِكَ نُنْجِيْ الْمُؤْمِنِيْنَ وَ صَلَّى اللّٰهُ عَلٰى مُحَمَّدٍ وَ اٰلِهِ الطَّيِّبِيْنَ الطَّاهِرِين. Wannan ana so mutum ya karanta kullum sau 10, don maganin masibobin da ke aukuwa. Da kuma sauran addu'o'i ruwaitattu na kade masifofi. Nahisa gaskiya ne, don Allah (T...

Hirar jaridar dailytrust tare da Sheikh zakzaky a Shekarar 2009

Image
 WATA HIRA DÀ SHEIKH IBRAHIM ZAKZAKY (H) YAYI DA JARIDAR DAILY TRUST A  10/10/2009.  TRUST: Kwamishinan ’yan sanda na jihar Kaduna, Tambari Yabo, an jiyo shi yana cewa  duk da cewa an hana duk wata zanga-zanga ta addini, a taron su na Kwamitin tsaro  an ce musu su kyale mabiyanka su yi zanga-zangarsu, kana ganin gwamnatin ba za ta iya  dakatar da ku bane cikin sauki, dama kuma wasu na ganin cewa gwamnati ba za ta iya iko  da kai da mabiyanka ba, kana jin wannan shi ne  dalilin da ya sa Kwamitin tsaron ya zartar da shawarar  kyale ku ku yi zanga- zangarku duk da cewa an hana?  SHAIKH ZAKZAKY: To, ni dai ban da masaniyar wani hani da aka yi, ban taba jin an  hana wata muzaharar addini ba. Ban kuma taba sanin an kyale ba. Abin da muka sani shi ne  mun shafe shekaru 26 muna irin wannan jerinn gwano.  Muzahara ce ta nuna goyon baya ga Palasdinawa, kuma ana yin sa a kasashe da dama  na duniya. In ka kira shi na addini, kana...

DABARA TARAGE GA MAISHIGA RIJIYA

Image
  DABARA TA RAGE GA MAI SHIGA RIJIYA! A Cikin Sahihul Bukhari Mujalladi Na 9 Hadisi Mai Lamba 214. Annabi(S.A.W.) Yayi Addu'a Ga Kasar SHAM (Syria) Da Kasar Yemen. Sai Wasu Mutane Suka Ce:"Ya Rasulullahi (S.A.W) Ka Hada Da Najadu Mana  Sai Bai Ce Musu Komai Ba. An Yi Haka Har Sau Uku. Sai Annabi(S.A.W.) Ya Ce Ba Zan Yi Addu'a Ga NAJAD Ba, Domin Girgizar Kasar Musulunci Da Masifu Zasu Kunno Kai Daga Nan Najdu. Kuma Kahon Shaitan/Dujjal Acan Zai Fito". SADAQAL RASULUL KAREEM!!! To Yau Dai Akwai Wani Hamshakin Malami Wanda Ba Sai Na Fadi Sunan Shi Ba Kowa Ya San Shi, Wanda Ake Masa Lakabi Da Wannan Sunan Garin AL- NAJDI, Inda Daga Bahaguwar Akidarsa (wato Wahabiyanci/ Salafiya) Ne Aka Samu Kungiyoyi Kamarsu: Al- Qa'eeda, Taliban, Al-Shabab, Ansaruddeen, Izala da Sauransu. . Inda Kullum Ba Abinda Suke Sai Shafawa Musulunci Da Musulmai Bakin Fenti, Kadan Daga Cikin Aika Aikansu Shine Su Kashe Musulmi Murus Da Sunan Jihadi Su Bar Kafiri/ Arne Yana Yawo a Doron Kasa Suna...

MAZA SUN DAWA SAI NISA.

Image
 *ALKALAMI KA FI REZA KAIFI* M. I. GAMAWA 07035577745  Dukkan alamu sojojin Najeriya sun hadiyi tabarya. Kamar yadda Bahaushe ke cewa, “wanda ya hadiyi tabarya tsaye zai kwan,” Sojojin Najeriya sun fahimci jini duk jini ne, amma banda na dan Sarki. Sun sha aikata danya su tsira babu mai tuhumar su. Kama daga yakin Basasa zuwa ta'addancin gidan Fela da ya jawo mutuwan mahaifiyarsa, matar da ta fara tuka mota a Najeriya, zuwa Zaki Biam da Udi da ke jihar Benuwe da Bayalsa a tartibance. Haka ya sa girman kansu ya karu, dagawa ta yawaita, rashin hankali ya wuce na mai shiga turu. Da ma suna jiran Soja a farar hula domin ci gaba da aikata mugun aikin da suka saba na kashe ’yan kasa da azabta su. Ilai kuwa sai ga Buhari, wanda babu tausayi, babu ragowa balle imani a zuciyarsa. Ganin na gida ya samu sai suka fahimci, Tula ba ta rabu da Kalaye ba, suka bude kofar muguntan da suka rufe a sakamakon dawowar dimokradiyya. Shi kuma Buhari ya jinjina musu bisa wannan danyen aiki nasu. Bai d...

AL-BISHIRINKU

Image
 ALBISHIRINKU!  Cibiyar Wallafa Ayyukan Jagora, Shaikh Zakzaky Na Gabatar Muku Da Sabon Littafi Mai Suna: “DA’AWAR HARKAR MUSULUNCI” (Karkashin Jagorancin Shaikh Ibraheem Zakzaky) Littafin wanda ke da shafuka 400, shine mafi girman littafi da aka wallafa da ke dauke da bayanan Tarihin Harkar Musulunci zuwa yanzu. Ya kunshi muhimmai kuma gamsassun bayanai dangane da Asalin Da’awar Harkar Musulunci da Musabbabi ko dalilinta, Hadafi da Manufarta, Tarihi da Nizaminta, Ayyuka da Harkokinta, Cibiyoyi da Mu’assasosinta, Fitintinu da Waqi’o’inta. Littafin Da’awar Harkar Musulunci na dauke da babuka 17, fasulla 120 da kuma kalmomi dubu 85,000, ya kunshi hotunan Tarihi a wasu babukan da suke bukatar mai karatu ya ga hoton abin da ake magana a kai.  Bayan gabatar da bayanai kan lalurar da ta sa aka rubuta littafin a daidai wannan lokacin wanda ya hada da yadda makiya Harkar Musulunci ke ta kokarin samar da rubuce-rubuce da littafai da ma fima-fimai a kan Harkar Musulunci ta fuskar d...

DDALILIN DA YASA MUKA CE AKORI SHARI'AR DA AKE MA MALAM ZAKZAKY(H)

Image
 Abin da ya sa muka nemi a kori shari’ar da ake wa Malam [H] – Barista Ishak Adam Barista Ishaka Adam na cikin Lauyoyin da ke tsaya wa Shaikh Ibraheem Zakzaky a karar da gwamnatin Jihar Kaduna ta shigar da shi shekaru biyu da suka gabata. A cikin wannan hirar da suka yi da Aliyu Saleh, fitaccen Lauyan ya bayyana dalilansu na shigar da bukatar kotu ta yi watsi da shari’ar da ake yi wa Shaikh Zakzaky da maidakinsa Malama Zeenah. Sannan ya bayyana abin da suke fatan samu a hukuncin da kotun za ta yanke ranar Talata 29 ga Satumba mai zuwa. ALMIZAN: Masu karatu za su so sanin abin da ya sa Lauyoyin Shaikh Zakzaky suka shigar da kara suna neman kotu ta yi watsi da shari’ar da ake yi masa wacce aka kwashe sama da shekaru biyu ana yi? BARISTA ISHAKA ADAM: Sakamakon gwamnatin Jihar Kaduna ta shigar da su Malam Zakzaky kara tana tuhumar su da aikata wasu laifuffuka guda takwas tun a watan Yuni na 2018, wanda aka fara shiga kotu a ranar 5 ga wata, har ya zuwa yanzu fiye da shekaru biyu ke nan...

YUNƘURIN ZUBAR DA JINI. yakamata ɗan'uwa yayi kyakykyawan shiri.

Image
 Me Zasuyi Nan Gaba? Allahu A'alamu:-  SABODA HAKA MUTUM YAYI KYAKKYAWAN SHIRI DAGA NAN ZUWA ARBA'EENA—Shaikh Yakubu Yahaya Katsina. "Sai su ce ai dan an tare hanya ne, shin hukuncin tare hanya shi ne ayi ma mutum abinda akayi wa Su Malam? Ko kuma suce ai dan ana zagin sahabbai ne to dama ita gwamnatin ta kare sahabbai ce? Kuma a kawo mana jawabi 1 ko inda jagoranmu Malam Ibraheem Zakzaky (H) ya zagi wani sahabi... Saboda haka su 'yan'uwa kada suyi tunanin ba zasu kara ba, a'a shirye suke su kara, Allah kadai kuma Ya san miye tanadinsu, tunda sunje wata jaha sunyi taro kwanannan taron sirri irin wanda sukayi wancan lokacin wanda suna gama taron suka afka ma Malam a Zariya. To sun kara yin irin wannan taron kwanannan. To kaga mi zasuyi nan gaba Allahu A'alamu, kaga ashe ba bari sukayi ba, ba kuma shirye suke su bari ba. Illa dai kamar yadda nace ta namu bangare din mu dauki 'Ayyi Ihtimal' (Any Possibility) in Allah Ya rayar da mu falillahil hamdu, ya...