Posts

Hana Bara Ko Almajiranci: Shaikh Yakubu Yahaya Katsina Ya Maganta Tare Da Ba da Mafita Akan Haka.

Image
A cikin wasu Jawaban Maulidai da shahararren Malamin Addinin Musuluncin nan kuma wakilin 'yan uwa musulmi Almajiran Ibraheem Alzakzaky da ke a Jihar Katsina,Shaikh Yakubu Yahaya ya yi a kwanakin baya a loacin da aka soma rufe wasu makarantun horo da gyara tarbiya a Katsina,Daura da Kano bisa zargin ana abubuwan assha a wadannan cibiyoyi,Malamin ya maganta tare da aike wa da sako mai dauke da samar da mafita ga hukumomi akan kokarinsu na dakile bara ko almajiranci a jihohi da ma kasa baki daya. Duk mabambantan Jawaban nasa,Malamin ya kuma bayyana ra'ayinsa da yadda yake kallon za a magance wannan matsala tsakanin 6angarorin biyu;hukuma da kuma su masu bara ko almajirancin Ga dai wani yanki na Jawaban nasa da muka gutsuro maku: “To abin da muke kallon wannan(rufe makarantun Allo) shi ne mukaddima na rufe makarantun Allon duk kasar nan baki daya.Domin yanzu abin da gwamnati ke 6a6atu akan shi shine makarantun allo sun dame su da bara;ba su son bara. Ba mu ce bara addini ne...

DANGANE DA WATAN RAJAB

Image
*DANGANE DA WATAN RAJAB* *Daga Shaikh Ibraheem Zakzaky (H)* Rajab, idan mutum ya duba Mafatihul Jinan, a yayin da yake kawo ayyukan shekara ya fara da watan Rajab ne. Yana cewa; shi ne kamar watan farko a ayyuka.  Rajab, Sha’aban, Ramadan, watanni masu ayyuka na ibada. Saboda haka ya kamata mutum ya yi shirin shiga Rajab. Akwai ayyuka na musamman na daren farko na Rajab. Kar mutum ya yi sake. Daren farko da kuma, musamman azumin farkon Rajab din. Ya tashi da azumi daya ga watan Rajab. Da Rajab da Sha’aban da Ramadan, watanni ne masu darajar gaske. An samo hadisai daban-daban a kan falalolinsu. A cikin Ikbal A’amal, na ga shi Sayyid bn Dawus ya kawo wani dogon magana a kan cewa; ka sani dangane da falala an samo ruwayoyi da yawan gaske. To, ko da a ‘ka’idatul man balagah’. Idan ka san wata ka’ida ana ce ma ta ‘ka’idatul man balagah,’ hadisi ne aka samu daga A’imma daban- daban ma. An samu daga Imam Bakir da Imam Ja’afar da Ai’mma (AS) daban-daban ce...

WAYASANI MA KO RASHIN GYARUWAR MU KE DAKATAR DA FITOWAR SU MALAM

Image
Waya Sani ma Ko Rashin Gyaruwar Mu Ke Dakatar Da Fitowam Su Mallam (H) Din? Eh, to! maganan Gaskiya, kowanne cikin mu yasan abinda ke aikatawa a boye a hasken rana ko cikin duhu. Yau da ace a tara dukkanin matasan wannan harkar wadanda suke Dass, Bauchi, Kano, Katsina Abuja da Sokoto dama Zariya da Kaduna dama dukkan sauran yankunan kasar nan, bansan yawan mu ba amma nasan lissafin Miliyoyi za'ayi kuma tabbas munkai haka. Ba ina magana yara bane, a'a matasa da suka mallaki hankalin su. Ace mana kowannen mu ya biya hakkin shuhada da ake binshi bashi na baya, wallahi da zamu biya, adadin kudin zai iya sayan babban mota da Jari dukkan iyayen Shahidan harkar nan duka! Kuma yabada dama a biya kudin makarantan 'ya'yan Shahidai su zama lauyoyi da Injiniyoyi da likitoti wallahi ba wasa nake ba. Amma meke faruwa? Bamu da kudin ne? A'a kawai bamu gama yarda gaskiya muke kai ba. Kuma bamu girmama maganan Jagoran harkar. Nasan akwai iyaye a cikin mu, ko kaine akace maka w...

MALA'IKA JIBRILU SAIDA YA SHAWARA NB DA ANNABI LOKACIN DA ZAI FARA YIMASA WAHAYI. Ba maƙure shi yayi ba

Image
"Mala'ika Jibrilu sai da ya nemi Izinin manzon Allah ranar da ya fara kawo mashi sako,ba makure shi yayi ba" -Shaikh Yakubu Yahaya Katsina. Daga Auwal Isa Musa. A cikin Jawabin da Malamin Addinin Musuluncin nan a 6angaren 'yan uwa Musulmi almajiran Shaikh Ibraheem Yaqoub Alzakzaky na Katsina, Shaikh Yakubu Yahaya ya gabatar a ranar Lahadin nan na tunawa da ranar Yaumul-mub'ath wato ranar da aka fara aiko manzon Allah(S) da Sako zuwa ga Talikai,Malamin yace; Mala'ika Jibrilu(A.s) bai ta6a razana manzon Allah(S) balle makureshi ko kuma wahalar da shi ba tun da yake zuwa kawo masa sako,bilhasali ma yana neman izininsa ne a duk lokacin da yazo garesa. Malamin ya kara da cewa; a lokacin da Manzon Allah ya kai shekara Arba'in. sai Allah ya turo mala'ika Jibrilu da sakon Annabta da Ayar nan ta 'Ikra'a,amma da yazo ya sami Manzon Allah a kogon Hira sai da ya nemi izin shiga wajensa,ba matse shi yayi ba:  "Wata ruwayar a falke (Jibrilu) ya ...

NIFA ABINDA ZANCE SAIDAI AYI HAƘURI DANI- Bilya Hamza Dass

Image
Angama Maganan Kotu Ko? To Ni Ga Abinda Zance, Sai Dai Ayi Hakuri Dani. Abokin ku, Bilya Hamza Dass Nagama ganin 'yan uwa sunyi ta kawo rahotannin abinda yafaru a kotu yau harda zuwa hutu da kuma dawowa da yanda aka kare har bada doka ta biyu da Alkali ya bayar na cewa lalle abaiwa likitotin su Mallam daman ganin su ko yaushe. Tare da maganan sake sanya watarana da akace kamar 23 da 24 na watan 4 domin cigaba da zaman! Toh! Allah yafada a littafin shi me tsarki cewa; baze taba daura kafirai akan masu imani ba. Wani wajan yace; 'Hakki ne akan mu mu temaki masu imani' (Aya). To gashi munyi imani kuma har mun zamu “Victims” na imanin mu ga Allah ta'ala kuma gashi azzalumai nata kadamu da cutarwa menene ke faruwa? Karka raba 1 zuwa 2, magana ta Allah bamu shirya tsakanin mu da Allah bane. Ranar wanka be kamata ayita boye ciki ba, domin shima yana bukatan a wanke shi. A baya muna hangen munanan ayyuka daga wajen mu muna bada misalai dasu muna gujewa tare da addu'...

TARON MATASA KARO NA 27 A GARIN BAUCHI- Nasihohin Sheikh yaqub yahya katsian.

Image
Taron Matasa Karo Na 27 A Garin Bauchi: Rahoto Na Biyu: Nasihohin Sheikh Yakubu Yahaya Ga Matasa Daga Bilya Hamza Dass “Ba sai anzo wajan taro (Mu'utamar) kafin a dinga tashi ana sallar dare ba, wannan wani abu ne muhimmi, hasalima yana daga cikin manyan alamomi da ake gane mumuni” inji shi. A wani bangare na jawabin nashi babban bako me jawabi a wajan Sheik Yakubu Yahaya yaja hankalin matasa wajan kula da Ibada musamman a shekarun su na matasan taka. Yace “Abinda su Mallam suke so shine su samar da wasu mutane wadan da Allah zai damka musu amanar al'umma, wadanda zasuce Allah yayi kuma yayin” kuma wannan alkawari na shi. Yakawo misalai yanda Allah yake zabar wasu dai-daikun bayin shi ya damka musu amanar al'umma, yayin da yaga tsaran su greshi da kuma amanar su. Misali Imam Kumai ni (R) da Shehu 'Dan Fodiyo wadanda wadanan sun faru shekaru kadan baya. Yace to wannn shine hankoron su Mallam (H) yace ya bayyana ba sau daya ba, cewa babbn gudumawa da wani zai baya...

KWANAKIN DA AKA SHIGA KOTUN SU SHEIKH ZAKZAKY A TSAWON SHEKARA BIYU

Image
KWANAKIN DA AKA SHIGA SHARI'AR SHAIKH ZAKZAKY A TSAWON SHEKARU BIYU 1— 15/5/2018 2— 21/6/2018 3— 2/8/2018 4— 4/10/2018 5— 7/11/2018 6— 22/1/2019 7— 25/3/2019 8— 18/7/2019 9— 29/7/2019 10- 5/8/2019 11- 5/12/2019 12- 6/2/2020 An shiga shari'ar sau 12, kuma an je da su Shaikh Zakzaky da mai dakinsa kotun sau kusan 5, a yayin da zama 7 ba su halarta ba, saboda yanayoyin jikinsu. Ko da yake so daya ba a yi zaman kotun ba, a ranar da aka ce Keke Napep ya mangare Alkalin. Duk wadannan kwanaki 12 din a tsawon shekara biyu har yanzu ba a fara gabatar da shari'ar ba. Kamar yadda ma kowa ya sani, sai gobe Litini da Talata ne za a cigaba da shari'ar, inda wai ake sa ran za a karantowa su Shaikh Zakzaky tuhumar da ake musu su amsa ko su kore shi. Kafin a fara shari'a. Tabbas tarihi zai rubuta ya kuma taskace duk wani nau'in zalunci da azzaluman mahukuntan Kasar nen ke yi wa Shaikh Ibraheem Zakzaky da almajiransa, ba abin da za a manta ko a bar shi ya bace,...