Posts

Muzaharorin Qudus: Dubun-dubata Suka Halarta A Katsina

Image
Muzaharorin Qudus: Dubunnai Suka Shiga A Katsina. @Daga A.I Musa Voice of Sheikh Kamar yadda duk duniya a juma'ar karshen watan Ramadhan na kowace shekara, Musulmin duniya kan gudanar da Muzaharorin nuna goyon bayansu ga Palasdinawa daga cin zarafin da Isra'ila ke yi ma su a kullum, bana ma, 'yan uwa Musulmi almajiran Shaikh Ibraheem Yaqoub Alzakzaky(H) na garin Katsina a tarayyar Nijeriya, sun bi sahun tagwarorinsu Musulmin na sauran Kasashe, wajen gudanar da jerin goyon bayan Palstinawan. Jerin gwanon Muzaharar wanda ya fara da misalin Karfe 9:00 daidai na safiyar Juma'ar nan 25 ga Ramadhan 1442H (7 ga Mayu, 2021) ya samu halartar dubun-dubatar al'ummar Musulmi. Muzaharar dai ta tashi daga Unguwar Madawaki inda kaitsaye da wuce zuwa Babban Masallacin Juma'a, ta kuma karkata ta bi ta Mobil, ta zagaya ta zo Sabon layi, inda aka tuke ta Tashar Gagare. A lokacin gudanar da Muzaharar, dinbin al'umma ne dauke da hotunan Palasdinawa da hot...

YAKIN BADAR BABBAR NASARACE GA MUSULUNCI

Image
Yakin Badar Babbar Nasara Ce Da Ke Tabbatar Da Kafuwar Daular Musulunci, Inji Farfesa Danladi Daga Ammar M. Rajab Farfesa Abdullahi Danladi, Malami a Jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya ya bayyana cewa yakin Badar babbar nasara ce da ke tabbatar da cewa daular Musulunci ta kafu babu mai iya nuna mata dan yatsa. Farfesan ya bayyana hakan ne a yayin muhadara kan ranar Badar da ya gudana a jiya Alhamis 17 ga watan Ramadan 1442 a garin Zariya. Taron ya gudana ne a muhallin Fudiyya dake Babban Dodo Zariya. A kowacce rana cikin watan Ramadan, ana gudanar da Tafsirin Alkur’ani mai girma wanda Shaikh Abdulhameed Bello ke jagoranta, sai dai a jiyan an gudanar da muhadara ce kan ranar Badar wanda Farfesa Abdullahi Danladi ya gabatar da jawabi.  Farfesa Abdullahi Danladi ya kawo tarihin yakin Badar tiryan-triyan, harma ya nuna yadda tun daga yakin Badar da aka yi, aka samu fasahar amfani da ‘camouflage’ da dakarun sojoji suke amfani da shi a yau.  A wani bangare na jawabinsa, Fa...

SHAIKH YAƘUBU YAHAYA YA YI WA RAUNI KASHEDI.

Image
SHAIKH YAƘUBU YAHAYA YA YI WA RAUNI KASHEDI.  An buƙaci 'yan uwa da kada su sakar wa rauni fuska har su ɗauka cewa akwai abinda basu iyawa. Shaikh Yaƙub  Yahaya ya bayar da wannan shawarar alokacin da yake jawabi  alokacin da 'Yan lajnar islamiyyu suka kaimasa ziyarar shekara - shekara da suka saba kaimasa.  Malamin ya bayar da misali da lmam Khumaini alokacin da aka kafa daula aka rasa masu gyaran jiragen sama,  saboda ɓarnar da Amerikawa sukayi a ƙasar inda ya buƙacesu da suje su gyara jiragen zasu iya.  Da kuma misalin Fital castro na cuba wanda ya ɗauki ƙarfafa ilimi musamman na likitoci,  da injiya, a matsayin hanyar fitar da ƙasarsa daga cikin ƙunci da maysaloli. Malamin ya yi kira ga Malaman islamiyyu da suƙara zage damtse wirin ba 'ya 'yan 'yan uwa karatu sosai musamman akan Ƙur'ani da Tajwid,   sai Tauhid,  da Akhlaƙ.  Waɗannan sunada mahimmaci sosai ga al'umma.  Shaikh Yaƙub Yahaya ya bayyana haka ne aloka...

SHEIKH ZAKZAKY; Bayan kammala jami'a

Image
— Bayan Kammala Jami’a: Daga: Cibiyar Wallafa da Yaɗa Jawaban Shaikh Ibraheem Zakzaky (H).  Bayan kammala Jami’a, Shaikh Zakzaky ya cigaba da gabatar da gwagwarmayarsa na yunkurin tabbatar da addinin Musulunci. Tun a shekarar ta 1979 ta bayyana balo-balo cewa akwai wata da’awa da ke kira a komawa tsarin addinin Musulunci. Sai dai tana jami’a ce kawai a tsakanin daliban jami’a, amma a waje ba a san da ita ba. Ana wannan halin ne, kawai sai ga juyin-juya halin Musulunci na Iran a watan February 1979. Ga wani Malamin addinin Musulunci ya kira mutane zuwa ga komawa nizamin Musulunci, kuma ya fafata tsawon shekaru, har yau gashi ya juya kasar ya kori nizamin kafirci ya tabbatar da na Musulunci. Wannan ya karawa Shaikh Zakzaky da masu ra’ayinsa kwarin guiwa sosai, cewa lallai wannan abin da suke da’awarsa mai yiwuwa ne in har sun dake. Juyin Musulunci na Iran ya kuma ba da amsa ga masu ganin cewa ba zai yiwu addinin Musulunci ya dawo yai iko da mutane ba, a yayin da ga wani M...

SHEKARARSA 70 A DUNIYA...A cikin wannan shekarun ya kwashe da yawansu cikin Ibtila'I na zalumcin azzalumai- Rahama Abdulmajid

Image
SHEKARARSA 70 A DUNIYA... A cikin wannan shekarun ya kwashe da yawansu cikin Ibtila'I na zalumcin azzalumai. 1 Shekara shida kenan da aka daure shi daga shi har matarsa  2 A cikin wannan shekarunsa Saba'in Gwamnatoci suka karar da 'ya'yansa. 3 A cikin wannan shekarun an kashe dubban mabiyansa maza da mata manya da yara har da na goye da suke asalin yan Najeriya masu hakkin tsaro da kare lafiya a wuyan gwamnati. 4 A cikin wadannan shekarun aka rushe duk wani waje da ya mallaka  5 a cikin wannan shekarun ne Kotu ta rika bayar da belinsa gwamnati na take umarnin kotu. 6 A cikin wannan shekarun duka bai kira mabiyansa da su dauki makami kamar yadda inyamurai ke dauka su kwana lafiya, yarbawa ke dauka su kwana lafiya, Fulani ke dauka su kwana lafiya.  7 Laifinsa daya shine ya zabi hanyar da ya ke ganin ita ce addininsa a kasar da kundin tsarin mulkinta  yace kowa na da 'yancin yin addini yadda yake so cikin walwala. DA INA DA DAMAR BAYAR DA AWARD HAKIKA ZAN B...

Kasar Allah Sheikh Zakzaky yakeso ya kafa, kuma sai ta kafu Daram

Image
KASAR ALLAH SHAIKH ZAKZAKY KE SON YA KAFA, KUMA SAI TA KAFU DARAM!  — Inji Shaikh Yakubu Yahya Katsina a wajen Nisfu Sha'aban 1442H.  "Abin da mutane ba su fahimta ba shine, Malam Zakzaky (H) kasar Allah yake so ya tabbatar. Addinin Allah a cikin bayin Allah shine abin da Malam Zakzaky ke son ya tabbatar. Kuma bai tilastawa kowa sai ya yi ba. Mutane suna ganin kamar abin da Malam ke kira ba zai taba yiwuwa ba, ko kuma suna da wani dalili, kamar su ce ya za a yi ai kasar ba ta Musulmi bace gaba daya, akwai kiristoci da Maguzawa da sauransu, in aka ce za a yi Musulunci to akwai matsala. "Na yi magana da wani irin haka nan, sai nace masa ai muna magana ne a kan Kasar Allah ba kasar Bature ba, kai kana magana a kan kasar Bature mai kan iyakoki yamma da kudu, arewa da gabas da central government. In ita kake magana a kai, to shi Malam na magana ne a kan kasar Allah da yace "Inna ardhiy wasi'a fa'iyyaya fa' abuduniy", ita Malam ke magana a kai....

HOTUNA; Yanda aka gudanar da Bikin tunawa da Ranar Haihuwar Imam Mahadi da Sayyid Zakzaky a katsina

Image
Hoton yadda aka gabatar da Walimar Nisfu Sha'aban a Garin Katsina. Daga Adam Lawal Litanin 29/03/2021 Yan uwa Almajiran Shaikh Zakzaky (h), dake Birnin katsina yayi gabatar Taron Tunawa da Ranar Haihuwar Imam Mahdi (AF) tare da Sayyid Zakzaky (h). Irin wannan wata na Sha'aban 15 ga wata ne aka haifi Imam Mahdi tare da Malam Zakzaky. Mun hadu ne domin taya su Murna tare da sauraren Jawabin Falalolinsu da kuma darajarsu. Shaikh Yaqoub Yahya ne ya jagoranci zaman tare da Jawabi akan Rayuwar Malam Zakzaky da irin baiwarsa. An gabatar da wannan walima a Markaz din yan uwa dake Katsina tare da Yanka Cake duk dan Murna da Ranar haihuwarsa.