AL'MAJIRAN SHEIKH ZAKZAKY 38 GWAMNATIN BUHARI TA KASHE ACIKIN SHEKARAR DATA GABATA 2019

ALMAJIRAN SHAIKH ZAKZAKY 38 JAMI’AN TSARO SUKA KASHE A SHEKARAR 2019 Daga Saifullahi M. Kabir A yayin da shekarar Miladiyya ta 2019 ke karewa a yau Talata, muna tunawa da irin ta’addancin gwamnatin Buhari a kan ‘yan uwa Musulmi almajiran Shaikh Zakzaky (H), wanda ya sabbaba samun Shahidai akalla 38 a cikin wannan shekarar. A ranar 9/7/2019 ne ‘yan sanda suka bude wuta a kan masu muzaharar kira a saki Shaikh Ibraheem Zakzaky, inda suka kashe mutane biyu a kofar majalisar tarayyar Nijeriya a garin Abuja. ‘Yan uwan da suka kashe a wannan ranar sune Shahid Jafar Mika’il Lafiya da Shahid Mahmud Umar Suleja. Bayan kwana uku da wannan waki’ar a ranar 11/7/2019 kuma ‘yan sanda suka kuma budewa masu muzahar kira a saki Shaikh Zakzaky din a garin Kaduna, inda suka kashe ‘yan uwa Musulmi guda biyu; Shahid Ahmad Nasir da Shahid Abubakar Aliyu Badikko. Kwanaki biyar bayan hakan, a ranar Talata 16/7/2019 ‘yan sanda suka kuma aukawa masu muzaharar kira a saki Malam Zakzaky a Kaduna, inda su...