Hana Bara Ko Almajiranci: Shaikh Yakubu Yahaya Katsina Ya Maganta Tare Da Ba da Mafita Akan Haka.

A cikin wasu Jawaban Maulidai da shahararren Malamin Addinin Musuluncin nan kuma wakilin 'yan uwa musulmi Almajiran Ibraheem Alzakzaky da ke a Jihar Katsina,Shaikh Yakubu Yahaya ya yi a kwanakin baya a loacin da aka soma rufe wasu makarantun horo da gyara tarbiya a Katsina,Daura da Kano bisa zargin ana abubuwan assha a wadannan cibiyoyi,Malamin ya maganta tare da aike wa da sako mai dauke da samar da mafita ga hukumomi akan kokarinsu na dakile bara ko almajiranci a jihohi da ma kasa baki daya. Duk mabambantan Jawaban nasa,Malamin ya kuma bayyana ra'ayinsa da yadda yake kallon za a magance wannan matsala tsakanin 6angarorin biyu;hukuma da kuma su masu bara ko almajirancin Ga dai wani yanki na Jawaban nasa da muka gutsuro maku: “To abin da muke kallon wannan(rufe makarantun Allo) shi ne mukaddima na rufe makarantun Allon duk kasar nan baki daya.Domin yanzu abin da gwamnati ke 6a6atu akan shi shine makarantun allo sun dame su da bara;ba su son bara. Ba mu ce bara addini ne...