Posts

Sheikh Adamu Tsoho Jos Ya Cika Shekaru 60; Tarihin Sheikh Adamu Tsoho A Taƙaice !

Image
  Sheikh Adamu Tsoho Jos Ya Cika Shekaru 60 Tarihin Sheikh Adamu Tsoho A Taƙaice ! Sheikh Adum Tsoho Jos (Malamin Addinin Musulunci Yau 21-Feb-2021 yayi daidai da ranar zagayowar Haihuwar Sheikh Adamu Tsoho Jos, kuma an haifi Shaikh Adamu a garin Jos ta jihar Plateau, ranar Alhamis 27 ga Ramadan 1382H daidai da 21/2/1962. Yau kimanin shekaru 59 kenan.  Mahaifinsa sunansa Malam Muhammad Sani, amma an fi kiransa da Tsoho, kakansa kuma Malam Ahmad Kiffa, wanda yana daya daga cikin mutane 14 da aka kwaso su daga Bauchi a wancan lokacin aka kawo su Jos da nufin su raya garin na Jos. Kamar yadda mahaifin Shaikh din ya tabbatar min a wani hira da na taba yi da shi a kan tarihin kafa garin Jos a kwanakin baya. Mahaifiyar Shaikh Adamu Tsoho kuwa sunanta Hajiya Amina, ba a fi shekaru 11 ba da Allah Ya mata rasuwa. A yayin da su goma ne a wajen mahaifinsu, sai dai mahaifin nasu ya tabbatar min da cewa Shaikh Adamu Tsoho na daban ne a cikin 'ya'yan nasa ta fuskacin tsayuwa da addini da ku...

Haihuwar Mai Albishi, Annabi Muhammad (S)

 Haihuwar Mai Albishir, Annabi Muhammadu (s) Daga Marigayi Muhd Awwal Bauchi Manzon Allah Muhammad bn Abdullah (s.a.w.a)  (A bisa ingantattun ruwayoyi), an haifi Manzon Allah (s) ne a ranar 17 ga watan Rabiul Awwal, ko da yake wasu ruwayoyin sun ce ran 12 ga wanann wata ne, a garin Makka, a shekarar da ake kira da Shekarar Giwaye. Dalilin da ya sa ake kiran wannan shekara da haka kuwa shi ne wani gwamnan Sarkin Abbasiniya ne mai suna Abrahata ya shigo Makka da runduna mai yawa bisa kan giwaye (bayan ya kame garin Yaman) da nufin rusa Dakin Ka'aba da sauya alkiblar mutane zuwa San'a (domin a wancan lokacin mutane sukan kawo ziyarar bauta a Ka'aba) inda da ma tuni ya gina wani guri don wannan ziyara. Amma daga baya lokacin da Abrahata ya iso Makka da wannan runduna ta sa, sai Allah Ya aiko da wasu irin tsuntsaye dauke da tsakuwoyi a bakunansu, inda suka rinka jefo wadannan tsakuwoyi a kan wadannan runduna, nan take suka kashe sojojin da giwayen. Ta haka ne Allah Ya yi magani...

Muzaharorin Qudus: Dubun-dubata Suka Halarta A Katsina

Image
Muzaharorin Qudus: Dubunnai Suka Shiga A Katsina. @Daga A.I Musa Voice of Sheikh Kamar yadda duk duniya a juma'ar karshen watan Ramadhan na kowace shekara, Musulmin duniya kan gudanar da Muzaharorin nuna goyon bayansu ga Palasdinawa daga cin zarafin da Isra'ila ke yi ma su a kullum, bana ma, 'yan uwa Musulmi almajiran Shaikh Ibraheem Yaqoub Alzakzaky(H) na garin Katsina a tarayyar Nijeriya, sun bi sahun tagwarorinsu Musulmin na sauran Kasashe, wajen gudanar da jerin goyon bayan Palstinawan. Jerin gwanon Muzaharar wanda ya fara da misalin Karfe 9:00 daidai na safiyar Juma'ar nan 25 ga Ramadhan 1442H (7 ga Mayu, 2021) ya samu halartar dubun-dubatar al'ummar Musulmi. Muzaharar dai ta tashi daga Unguwar Madawaki inda kaitsaye da wuce zuwa Babban Masallacin Juma'a, ta kuma karkata ta bi ta Mobil, ta zagaya ta zo Sabon layi, inda aka tuke ta Tashar Gagare. A lokacin gudanar da Muzaharar, dinbin al'umma ne dauke da hotunan Palasdinawa da hot...

YAKIN BADAR BABBAR NASARACE GA MUSULUNCI

Image
Yakin Badar Babbar Nasara Ce Da Ke Tabbatar Da Kafuwar Daular Musulunci, Inji Farfesa Danladi Daga Ammar M. Rajab Farfesa Abdullahi Danladi, Malami a Jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya ya bayyana cewa yakin Badar babbar nasara ce da ke tabbatar da cewa daular Musulunci ta kafu babu mai iya nuna mata dan yatsa. Farfesan ya bayyana hakan ne a yayin muhadara kan ranar Badar da ya gudana a jiya Alhamis 17 ga watan Ramadan 1442 a garin Zariya. Taron ya gudana ne a muhallin Fudiyya dake Babban Dodo Zariya. A kowacce rana cikin watan Ramadan, ana gudanar da Tafsirin Alkur’ani mai girma wanda Shaikh Abdulhameed Bello ke jagoranta, sai dai a jiyan an gudanar da muhadara ce kan ranar Badar wanda Farfesa Abdullahi Danladi ya gabatar da jawabi.  Farfesa Abdullahi Danladi ya kawo tarihin yakin Badar tiryan-triyan, harma ya nuna yadda tun daga yakin Badar da aka yi, aka samu fasahar amfani da ‘camouflage’ da dakarun sojoji suke amfani da shi a yau.  A wani bangare na jawabinsa, Fa...

SHAIKH YAƘUBU YAHAYA YA YI WA RAUNI KASHEDI.

Image
SHAIKH YAƘUBU YAHAYA YA YI WA RAUNI KASHEDI.  An buƙaci 'yan uwa da kada su sakar wa rauni fuska har su ɗauka cewa akwai abinda basu iyawa. Shaikh Yaƙub  Yahaya ya bayar da wannan shawarar alokacin da yake jawabi  alokacin da 'Yan lajnar islamiyyu suka kaimasa ziyarar shekara - shekara da suka saba kaimasa.  Malamin ya bayar da misali da lmam Khumaini alokacin da aka kafa daula aka rasa masu gyaran jiragen sama,  saboda ɓarnar da Amerikawa sukayi a ƙasar inda ya buƙacesu da suje su gyara jiragen zasu iya.  Da kuma misalin Fital castro na cuba wanda ya ɗauki ƙarfafa ilimi musamman na likitoci,  da injiya, a matsayin hanyar fitar da ƙasarsa daga cikin ƙunci da maysaloli. Malamin ya yi kira ga Malaman islamiyyu da suƙara zage damtse wirin ba 'ya 'yan 'yan uwa karatu sosai musamman akan Ƙur'ani da Tajwid,   sai Tauhid,  da Akhlaƙ.  Waɗannan sunada mahimmaci sosai ga al'umma.  Shaikh Yaƙub Yahaya ya bayyana haka ne aloka...

SHEIKH ZAKZAKY; Bayan kammala jami'a

Image
— Bayan Kammala Jami’a: Daga: Cibiyar Wallafa da Yaɗa Jawaban Shaikh Ibraheem Zakzaky (H).  Bayan kammala Jami’a, Shaikh Zakzaky ya cigaba da gabatar da gwagwarmayarsa na yunkurin tabbatar da addinin Musulunci. Tun a shekarar ta 1979 ta bayyana balo-balo cewa akwai wata da’awa da ke kira a komawa tsarin addinin Musulunci. Sai dai tana jami’a ce kawai a tsakanin daliban jami’a, amma a waje ba a san da ita ba. Ana wannan halin ne, kawai sai ga juyin-juya halin Musulunci na Iran a watan February 1979. Ga wani Malamin addinin Musulunci ya kira mutane zuwa ga komawa nizamin Musulunci, kuma ya fafata tsawon shekaru, har yau gashi ya juya kasar ya kori nizamin kafirci ya tabbatar da na Musulunci. Wannan ya karawa Shaikh Zakzaky da masu ra’ayinsa kwarin guiwa sosai, cewa lallai wannan abin da suke da’awarsa mai yiwuwa ne in har sun dake. Juyin Musulunci na Iran ya kuma ba da amsa ga masu ganin cewa ba zai yiwu addinin Musulunci ya dawo yai iko da mutane ba, a yayin da ga wani M...

SHEKARARSA 70 A DUNIYA...A cikin wannan shekarun ya kwashe da yawansu cikin Ibtila'I na zalumcin azzalumai- Rahama Abdulmajid

Image
SHEKARARSA 70 A DUNIYA... A cikin wannan shekarun ya kwashe da yawansu cikin Ibtila'I na zalumcin azzalumai. 1 Shekara shida kenan da aka daure shi daga shi har matarsa  2 A cikin wannan shekarunsa Saba'in Gwamnatoci suka karar da 'ya'yansa. 3 A cikin wannan shekarun an kashe dubban mabiyansa maza da mata manya da yara har da na goye da suke asalin yan Najeriya masu hakkin tsaro da kare lafiya a wuyan gwamnati. 4 A cikin wadannan shekarun aka rushe duk wani waje da ya mallaka  5 a cikin wannan shekarun ne Kotu ta rika bayar da belinsa gwamnati na take umarnin kotu. 6 A cikin wannan shekarun duka bai kira mabiyansa da su dauki makami kamar yadda inyamurai ke dauka su kwana lafiya, yarbawa ke dauka su kwana lafiya, Fulani ke dauka su kwana lafiya.  7 Laifinsa daya shine ya zabi hanyar da ya ke ganin ita ce addininsa a kasar da kundin tsarin mulkinta  yace kowa na da 'yancin yin addini yadda yake so cikin walwala. DA INA DA DAMAR BAYAR DA AWARD HAKIKA ZAN B...

Kasar Allah Sheikh Zakzaky yakeso ya kafa, kuma sai ta kafu Daram

Image
KASAR ALLAH SHAIKH ZAKZAKY KE SON YA KAFA, KUMA SAI TA KAFU DARAM!  — Inji Shaikh Yakubu Yahya Katsina a wajen Nisfu Sha'aban 1442H.  "Abin da mutane ba su fahimta ba shine, Malam Zakzaky (H) kasar Allah yake so ya tabbatar. Addinin Allah a cikin bayin Allah shine abin da Malam Zakzaky ke son ya tabbatar. Kuma bai tilastawa kowa sai ya yi ba. Mutane suna ganin kamar abin da Malam ke kira ba zai taba yiwuwa ba, ko kuma suna da wani dalili, kamar su ce ya za a yi ai kasar ba ta Musulmi bace gaba daya, akwai kiristoci da Maguzawa da sauransu, in aka ce za a yi Musulunci to akwai matsala. "Na yi magana da wani irin haka nan, sai nace masa ai muna magana ne a kan Kasar Allah ba kasar Bature ba, kai kana magana a kan kasar Bature mai kan iyakoki yamma da kudu, arewa da gabas da central government. In ita kake magana a kai, to shi Malam na magana ne a kan kasar Allah da yace "Inna ardhiy wasi'a fa'iyyaya fa' abuduniy", ita Malam ke magana a kai....

HOTUNA; Yanda aka gudanar da Bikin tunawa da Ranar Haihuwar Imam Mahadi da Sayyid Zakzaky a katsina

Image
Hoton yadda aka gabatar da Walimar Nisfu Sha'aban a Garin Katsina. Daga Adam Lawal Litanin 29/03/2021 Yan uwa Almajiran Shaikh Zakzaky (h), dake Birnin katsina yayi gabatar Taron Tunawa da Ranar Haihuwar Imam Mahdi (AF) tare da Sayyid Zakzaky (h). Irin wannan wata na Sha'aban 15 ga wata ne aka haifi Imam Mahdi tare da Malam Zakzaky. Mun hadu ne domin taya su Murna tare da sauraren Jawabin Falalolinsu da kuma darajarsu. Shaikh Yaqoub Yahya ne ya jagoranci zaman tare da Jawabi akan Rayuwar Malam Zakzaky da irin baiwarsa. An gabatar da wannan walima a Markaz din yan uwa dake Katsina tare da Yanka Cake duk dan Murna da Ranar haihuwarsa.

Sheikh Zakzaky a Shekuru 70

Image
SHAIKH ZAKZAKY A SHEKARU 70 Daga Saifullahi M. Kabir Kimanin shekaru 220, lokacin jihadin Shehu Usman Dan Fodiyo (RH) kakannin Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), suka dungumo suka zo kasar Hausa don su taimakawa wannan Mujaddadin na zamaninsu wajen kokarin tabbatar da addinin Musulunci a nahiyar yammaci. A wancan lokacin, kakan Shaikh Ibraheem Zakzaky na uku, mai suna Liman Husaini, wanda yake daya ne daga cikin Sharifan da ake kira Idrisiyyawa, tsatson Imam Hasanul Mujtaba (AS) ta hanyar Nafsuz-Zakiyya wadanda Umayyawa da Abbasiyawa da ma Wahabiyawa daga baya suka rabo kakanni da iyayensu daga yankin Larabawa suka fantsama zuwa sassan duniya, Allah ya kaddara zamansu a garin Shingidi da ke tsohuwar daular Mali ta da. Garin Shingidi, wanda yanzu an ce yana cikin Murtaniya ne, amma a da can duk kasashen suna karkashin wannan tsohuwar daula ta Malin da, wannan kakan na Shaikh Zakzaky ya kasance babban limaminsa.  Bayan sun baro garin Shingidi, sun rika zama a wasu garuruwa daba...

Limamin Zamani Imam Mahadi (AJ)

Image
LIMAMIN WANNAN ZAMANI; IMAM MAHDI (AJ) Daga Saifullahi M. Kabir Shine Imami na 12 kuma na karshe a jerin halifofin Manzon Allah shiryayyu goma sha biyu da Annabi (S) ya ce za su zo a bayansa. Shaikh Mufid a cikin Al’irshad ya kawo cewa, wanda ya kasance Imami a bayan Imam Hasan Al’askari shine Imam Mahdi (AS), wani bai gaji Imam Askari ba face shi, ya kasance shekarunsa biyar a lokacin wafatin mahaifinsa, Allah (T) ya sanya shi mai hukunci tun yana ƙarami kamar yadda ya sanya ga Annabi Yahya tun yana dan karami. Sannan kuma Allah ya sanya (Imam Mahdi) ya zama Imami a yayin da yake karami (dan shekaru 5) kamar yadda ya sanya Annabi Isa Dan Maryam ya zama Annabi tun yana tsumman goyo a jariri. Ruwayoyi daga Manzon Allah da Amirulmuminin da sauran A’imma Tsarkaka (AS) sun zo dangane da al’amarinshi. Shi ne ma’abocin takobi, tsayayye, wanda ake sauraro. Bayan haihuwar Imam Mahdi (AJ) ya shiga Ghaiba guda biyu, na farko mare tsawo, sannan bayan ita ya shiga mai tsawo wacce ya sh...

TAKAITACCEN TARIHIN ABUL FADALUL ABBAS; BABBAN GWARZO, JURUMI, DAN SADAUKI IMAM ALI(AS). KANIN IMAM HASAN(A.S) DA HUSAIN(AS):

Image
A ruwayar da ya fi shahara, an haifi Sayyid Abul Fadhl al-Abbas ne a garin Madina, a ranar 4 ga watan Sha’aban, shekara ta 26 bayan hijirar Annabi Muhammad(saw). Mahaifinsa dai shi ne Imam Ali Ibn Abi Talib(as), mahaifiyarsa kuwa ita ce Fatima bint Hazam bn Khalid bn Rabi’ ibn Amir Kalbi wacce aka fi sani da Ummul Banin, wacce ta fito daga kabilar Kilah, daya daga cikin mafiya daukakan daga cikin Bani Hashim da aka sansu da jaruntaka a fagen fama. Lokacin da labarin haihuwarsa ya kai ga mahaifinsa Imam Ali(as), Imam(as) ya yi sujada don nuna godiyarsa ga Allah Madaukakin Sarki. Bayan kwanaki bakwai da haihuwar, kamar yadda sunna ta tanadar Imam Ali(as) ya sanya wa wannan jariri suna Abbas. Tarihi ya tabbatar da cewa bayan shahadar Fatima al-Zahra(as), Imam Ali(as) ya bukaci dan’uwansa Akil da ya zaba masa wata mace wacce ta fito daga gidan ma’abuta jaruntaka don ya aura, don haka Akil ya zaba masa Fatima bint Hazam (Ummul Banin) don ya aure ta, haka kuwa lamarin ya kasance inda ya aure...

TAKAITACCEN TARIHIN IMAM HUSAIN(AS) DAN UWAN IMAM HASAN(AS); SHUWAGABANNIN SAMARIN AL-JANNAH.

Image
Nasabarsa ta bangaren mahaifinsa: Husain(as) dan Ali(as) dan Abi Talib(as) dan Abdul-mutallib…. Nasabarsa ta bangaren mahaifiyas: Husain(as) dan Fatimah(as) yar Annabi Muhammad(saw) dan Abdullah(as) da Abdul-mutallib…. Lakabinsa: Sayyidus- Shuhada, Ar-rashid, At-tayib, Al-Wafi, Az-zaki; As-sayyid, As-sa’id, Sibtis Sani, Tabi’u Li Mardhatillah, As-shahidu Bi Karbala, Dalil Ala Zatillah, Imamus Salis…. Alkunyarsa: Abu Abdillah. Ranar Haihuwarsa: Ranar Alhamis, 3 ga watan Sha’aban. Shekara ta 4 bayan Hijira. 10 January 626 M. Gurin Haihuwarsa: Garin Madina. Shekarunsa: 58. Farkon Imamancinsa: 28 Safar 50 H. 30 March 670 M. Tsawon shekarun imamancinsa: shekara 10. Ranar Wafatinsa: Ranar Juma’a, 10 ga watan Muharram, shekarata 61 H. 13 October 680 M. Dalilin Rasuwarsa: Rudunar sojojin Yazid dan Mu’awiya ne suka taru a kansa suka kashe shi da iyalan gidansa, a ranar Ashura, a Karbala. Gurin da kabarinsa: Garin Karbala (Iraq). Matansa: 1. Shahr ...

Ranar:28 November, 1989 (30 Rabius Thani, 1410H)

Image
Ranar: 28 November, 1989 (30 Rabius Thani, 1410H) A wannan ranar ne Shaikh Ibraheem Zakzaky ya fito daga kurkukun Fatakwal na kamun wakiar Kafancan, wanda Janaral Babangida ya yi masa.   Dama an kama Shaikh din ne a ranar 28 ga watan Maris 1987, sannan kuma aka yanke masa hukuncin dauri a ranar 28 ga Nuwambar 1987 din, don haka bayan shekara biyu cur da daure shi a ranar 28 ga Nuwambar 1989 aka sake shi. Shaikh Zakzaky ya fito bayan ya shafe shekaru biyu da wata takwas a tsare kenan. Kuma yana wannan kurkukun ne aka haifa masa yarsa ta biyu mai suna Nusaiba. — Daga littafin *Muhimman raneku 400 a Tarihin Harkar Musulunci*, na Cibiyar Wallafa.

DUK ACIKIN SAHABBAI IMAM ALI YAFI KOWA DARAJA

Image
Duk Cikin Sahabbai Imam Aliyu Yafi Kowa Daraja Bayan Manzon Allah (Saww).     Inji Sheikh Adamu Tsoho Jos.  Bayan bayyanar Annabcin Manzon Allah (Saww) daga wurin Ubangiji Allah Ta'ala, Sayyida Aliyu ne ya fara karban musulunci kafin sauran Sahabbai. Har ma yana cewa daga cikin kususiyyar daraja da Allah ya mishi, yayi Sallah tare da Manzon Allah  shekaru 7 tare da uwargidan Manzon Allah Sayyida Khadija a lokacin da babu wanda yake Sallah a duniya sai su. Da yawa yawancin mutane basu fahimci ƙadiya nasu Ahlulbait ba, wanda ake musu mummunar fahimta ta yadda duk abin da aka faɗa akan su sai mutane su ga ana fifitasu ne akan sauran Sahabbai. Shi yasa har yanzu kamar muna marhala ta farko ne na bayani akan su wanene Ahlulbait da matsayin su da kususiyya su. Idan muka koma tarihi zamu ga cewa da Manzon Allah (Saww) da Sayyida Aliyu tushen su ɗaya ne, asalinsu ɗaya ne. Menene asalin Manzon Allah (Saww)? Shine faɗin Allah (T) da yayi a cikin Alkur'ani ce wa, "A...

TAKAITACCEN TARIHI, HAIHUWA DA TASOWAR SHAIKH ZAKZAKY (H)

Image
Saura Kwanaki 15 Shaikh Zakzaky Ya Cika Shekaru 70 -Saifullahi M. Kabir TAKAITACCEN TARIHI, HAIHUWA DA TASOWAR SHAIKH ZAKZAKY (H) Ranar Talata 15 ga Sha’aban, 1372 aka haifi Jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), a unguwar Kwarbai da ke birnin Zariya ta jihar Kaduna. Mahaifinsa shine Malam Yaqoub dan Malam Ali dan Sharif Tajuddeen, shi kuma dan wani babban limami da ake kiransa da Liman Husaini. Kakan Shaikh Zakzaky na uku ya kasance daga cikin mutanen Shaikh Usman Danfodiye, wadanda ya tura su garuruwa a matsayin wakilansa, sai ya zama shi Malam Muhammad Tajuddeen Shaikh Danfodiye ya turo shi Lardin Zazzau ne a matsayin mai ba Amir din Zazzau, Malam Musa shawara da taimakonsa wajen tafiyar da harkokin al’umma akan tsarin Musulunci. A wata hira da aka yi da Shaikh Zakzaky dangane da tarihin rayuwarsa a shekarun baya, ya bayyana cewa: “Mahaifina Malamin Alkur’ani ne, haka ma kakana shima Malamin Alkur’ani ne, haka ma uban kaka na. Sai dai shi uban ...