HALIN DA ƘASA TAKE CIKI. ANRUFEWA SARAKUNA BAKI NE- Sultan Sa'ad Abubakar.

Halin da kasa ke ciki A Najeiya: ' An rufewa Sarakuna da Malaman Addini baki ' – Sarkin Musulmi Mai alfarma Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar, ya ce sarakuna da malaman addini da ya kamata su rika sanya ido kan shugabannin siyasa wajen suna yin abin da ya dace, an rufe musu baki. Sarkin Musulmi ya bayyana haka ne lokacin da yake jawabi a wajen taron Tattaunawa a Tsakanin Addinai kan Zaman Lafiya karo na Uku na bana da aka gudanar a Abuja. Taron ma taken “Tattaunawa a Tsakanin Addinai: Karfafa Al’adar Zaman Lafiya da Adalci da Sulhuntawa, Mai martaba Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II, ya wakilce shi a taron. Ya ce: “Duk wanda ya kashe wani Kirista ko Musulmi mai aikata babban laifi ne kuma a haka ya kamata a dauke shi. Duk abin da nake ji a yau mamaya ce. Sarakuna da shugabannin addini da ya kamata su sanya ido kan shugabannin siyasa don su aikata daidai ga jama’a, an tilasta su yin shiru. I...