Posts

Showing posts from March, 2021

SHEKARARSA 70 A DUNIYA...A cikin wannan shekarun ya kwashe da yawansu cikin Ibtila'I na zalumcin azzalumai- Rahama Abdulmajid

Image
SHEKARARSA 70 A DUNIYA... A cikin wannan shekarun ya kwashe da yawansu cikin Ibtila'I na zalumcin azzalumai. 1 Shekara shida kenan da aka daure shi daga shi har matarsa  2 A cikin wannan shekarunsa Saba'in Gwamnatoci suka karar da 'ya'yansa. 3 A cikin wannan shekarun an kashe dubban mabiyansa maza da mata manya da yara har da na goye da suke asalin yan Najeriya masu hakkin tsaro da kare lafiya a wuyan gwamnati. 4 A cikin wadannan shekarun aka rushe duk wani waje da ya mallaka  5 a cikin wannan shekarun ne Kotu ta rika bayar da belinsa gwamnati na take umarnin kotu. 6 A cikin wannan shekarun duka bai kira mabiyansa da su dauki makami kamar yadda inyamurai ke dauka su kwana lafiya, yarbawa ke dauka su kwana lafiya, Fulani ke dauka su kwana lafiya.  7 Laifinsa daya shine ya zabi hanyar da ya ke ganin ita ce addininsa a kasar da kundin tsarin mulkinta  yace kowa na da 'yancin yin addini yadda yake so cikin walwala. DA INA DA DAMAR BAYAR DA AWARD HAKIKA ZAN B

Kasar Allah Sheikh Zakzaky yakeso ya kafa, kuma sai ta kafu Daram

Image
KASAR ALLAH SHAIKH ZAKZAKY KE SON YA KAFA, KUMA SAI TA KAFU DARAM!  — Inji Shaikh Yakubu Yahya Katsina a wajen Nisfu Sha'aban 1442H.  "Abin da mutane ba su fahimta ba shine, Malam Zakzaky (H) kasar Allah yake so ya tabbatar. Addinin Allah a cikin bayin Allah shine abin da Malam Zakzaky ke son ya tabbatar. Kuma bai tilastawa kowa sai ya yi ba. Mutane suna ganin kamar abin da Malam ke kira ba zai taba yiwuwa ba, ko kuma suna da wani dalili, kamar su ce ya za a yi ai kasar ba ta Musulmi bace gaba daya, akwai kiristoci da Maguzawa da sauransu, in aka ce za a yi Musulunci to akwai matsala. "Na yi magana da wani irin haka nan, sai nace masa ai muna magana ne a kan Kasar Allah ba kasar Bature ba, kai kana magana a kan kasar Bature mai kan iyakoki yamma da kudu, arewa da gabas da central government. In ita kake magana a kai, to shi Malam na magana ne a kan kasar Allah da yace "Inna ardhiy wasi'a fa'iyyaya fa' abuduniy", ita Malam ke magana a kai.

HOTUNA; Yanda aka gudanar da Bikin tunawa da Ranar Haihuwar Imam Mahadi da Sayyid Zakzaky a katsina

Image
Hoton yadda aka gabatar da Walimar Nisfu Sha'aban a Garin Katsina. Daga Adam Lawal Litanin 29/03/2021 Yan uwa Almajiran Shaikh Zakzaky (h), dake Birnin katsina yayi gabatar Taron Tunawa da Ranar Haihuwar Imam Mahdi (AF) tare da Sayyid Zakzaky (h). Irin wannan wata na Sha'aban 15 ga wata ne aka haifi Imam Mahdi tare da Malam Zakzaky. Mun hadu ne domin taya su Murna tare da sauraren Jawabin Falalolinsu da kuma darajarsu. Shaikh Yaqoub Yahya ne ya jagoranci zaman tare da Jawabi akan Rayuwar Malam Zakzaky da irin baiwarsa. An gabatar da wannan walima a Markaz din yan uwa dake Katsina tare da Yanka Cake duk dan Murna da Ranar haihuwarsa.

Sheikh Zakzaky a Shekuru 70

Image
SHAIKH ZAKZAKY A SHEKARU 70 Daga Saifullahi M. Kabir Kimanin shekaru 220, lokacin jihadin Shehu Usman Dan Fodiyo (RH) kakannin Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), suka dungumo suka zo kasar Hausa don su taimakawa wannan Mujaddadin na zamaninsu wajen kokarin tabbatar da addinin Musulunci a nahiyar yammaci. A wancan lokacin, kakan Shaikh Ibraheem Zakzaky na uku, mai suna Liman Husaini, wanda yake daya ne daga cikin Sharifan da ake kira Idrisiyyawa, tsatson Imam Hasanul Mujtaba (AS) ta hanyar Nafsuz-Zakiyya wadanda Umayyawa da Abbasiyawa da ma Wahabiyawa daga baya suka rabo kakanni da iyayensu daga yankin Larabawa suka fantsama zuwa sassan duniya, Allah ya kaddara zamansu a garin Shingidi da ke tsohuwar daular Mali ta da. Garin Shingidi, wanda yanzu an ce yana cikin Murtaniya ne, amma a da can duk kasashen suna karkashin wannan tsohuwar daula ta Malin da, wannan kakan na Shaikh Zakzaky ya kasance babban limaminsa.  Bayan sun baro garin Shingidi, sun rika zama a wasu garuruwa daban-da

Limamin Zamani Imam Mahadi (AJ)

Image
LIMAMIN WANNAN ZAMANI; IMAM MAHDI (AJ) Daga Saifullahi M. Kabir Shine Imami na 12 kuma na karshe a jerin halifofin Manzon Allah shiryayyu goma sha biyu da Annabi (S) ya ce za su zo a bayansa. Shaikh Mufid a cikin Al’irshad ya kawo cewa, wanda ya kasance Imami a bayan Imam Hasan Al’askari shine Imam Mahdi (AS), wani bai gaji Imam Askari ba face shi, ya kasance shekarunsa biyar a lokacin wafatin mahaifinsa, Allah (T) ya sanya shi mai hukunci tun yana ƙarami kamar yadda ya sanya ga Annabi Yahya tun yana dan karami. Sannan kuma Allah ya sanya (Imam Mahdi) ya zama Imami a yayin da yake karami (dan shekaru 5) kamar yadda ya sanya Annabi Isa Dan Maryam ya zama Annabi tun yana tsumman goyo a jariri. Ruwayoyi daga Manzon Allah da Amirulmuminin da sauran A’imma Tsarkaka (AS) sun zo dangane da al’amarinshi. Shi ne ma’abocin takobi, tsayayye, wanda ake sauraro. Bayan haihuwar Imam Mahdi (AJ) ya shiga Ghaiba guda biyu, na farko mare tsawo, sannan bayan ita ya shiga mai tsawo wacce ya sh

TAKAITACCEN TARIHIN ABUL FADALUL ABBAS; BABBAN GWARZO, JURUMI, DAN SADAUKI IMAM ALI(AS). KANIN IMAM HASAN(A.S) DA HUSAIN(AS):

Image
A ruwayar da ya fi shahara, an haifi Sayyid Abul Fadhl al-Abbas ne a garin Madina, a ranar 4 ga watan Sha’aban, shekara ta 26 bayan hijirar Annabi Muhammad(saw). Mahaifinsa dai shi ne Imam Ali Ibn Abi Talib(as), mahaifiyarsa kuwa ita ce Fatima bint Hazam bn Khalid bn Rabi’ ibn Amir Kalbi wacce aka fi sani da Ummul Banin, wacce ta fito daga kabilar Kilah, daya daga cikin mafiya daukakan daga cikin Bani Hashim da aka sansu da jaruntaka a fagen fama. Lokacin da labarin haihuwarsa ya kai ga mahaifinsa Imam Ali(as), Imam(as) ya yi sujada don nuna godiyarsa ga Allah Madaukakin Sarki. Bayan kwanaki bakwai da haihuwar, kamar yadda sunna ta tanadar Imam Ali(as) ya sanya wa wannan jariri suna Abbas. Tarihi ya tabbatar da cewa bayan shahadar Fatima al-Zahra(as), Imam Ali(as) ya bukaci dan’uwansa Akil da ya zaba masa wata mace wacce ta fito daga gidan ma’abuta jaruntaka don ya aura, don haka Akil ya zaba masa Fatima bint Hazam (Ummul Banin) don ya aure ta, haka kuwa lamarin ya kasance inda ya aure

TAKAITACCEN TARIHIN IMAM HUSAIN(AS) DAN UWAN IMAM HASAN(AS); SHUWAGABANNIN SAMARIN AL-JANNAH.

Image
Nasabarsa ta bangaren mahaifinsa: Husain(as) dan Ali(as) dan Abi Talib(as) dan Abdul-mutallib…. Nasabarsa ta bangaren mahaifiyas: Husain(as) dan Fatimah(as) yar Annabi Muhammad(saw) dan Abdullah(as) da Abdul-mutallib…. Lakabinsa: Sayyidus- Shuhada, Ar-rashid, At-tayib, Al-Wafi, Az-zaki; As-sayyid, As-sa’id, Sibtis Sani, Tabi’u Li Mardhatillah, As-shahidu Bi Karbala, Dalil Ala Zatillah, Imamus Salis…. Alkunyarsa: Abu Abdillah. Ranar Haihuwarsa: Ranar Alhamis, 3 ga watan Sha’aban. Shekara ta 4 bayan Hijira. 10 January 626 M. Gurin Haihuwarsa: Garin Madina. Shekarunsa: 58. Farkon Imamancinsa: 28 Safar 50 H. 30 March 670 M. Tsawon shekarun imamancinsa: shekara 10. Ranar Wafatinsa: Ranar Juma’a, 10 ga watan Muharram, shekarata 61 H. 13 October 680 M. Dalilin Rasuwarsa: Rudunar sojojin Yazid dan Mu’awiya ne suka taru a kansa suka kashe shi da iyalan gidansa, a ranar Ashura, a Karbala. Gurin da kabarinsa: Garin Karbala (Iraq). Matansa: 1. Shahr

Ranar:28 November, 1989 (30 Rabius Thani, 1410H)

Image
Ranar: 28 November, 1989 (30 Rabius Thani, 1410H) A wannan ranar ne Shaikh Ibraheem Zakzaky ya fito daga kurkukun Fatakwal na kamun wakiar Kafancan, wanda Janaral Babangida ya yi masa.   Dama an kama Shaikh din ne a ranar 28 ga watan Maris 1987, sannan kuma aka yanke masa hukuncin dauri a ranar 28 ga Nuwambar 1987 din, don haka bayan shekara biyu cur da daure shi a ranar 28 ga Nuwambar 1989 aka sake shi. Shaikh Zakzaky ya fito bayan ya shafe shekaru biyu da wata takwas a tsare kenan. Kuma yana wannan kurkukun ne aka haifa masa yarsa ta biyu mai suna Nusaiba. — Daga littafin *Muhimman raneku 400 a Tarihin Harkar Musulunci*, na Cibiyar Wallafa.

DUK ACIKIN SAHABBAI IMAM ALI YAFI KOWA DARAJA

Image
Duk Cikin Sahabbai Imam Aliyu Yafi Kowa Daraja Bayan Manzon Allah (Saww).     Inji Sheikh Adamu Tsoho Jos.  Bayan bayyanar Annabcin Manzon Allah (Saww) daga wurin Ubangiji Allah Ta'ala, Sayyida Aliyu ne ya fara karban musulunci kafin sauran Sahabbai. Har ma yana cewa daga cikin kususiyyar daraja da Allah ya mishi, yayi Sallah tare da Manzon Allah  shekaru 7 tare da uwargidan Manzon Allah Sayyida Khadija a lokacin da babu wanda yake Sallah a duniya sai su. Da yawa yawancin mutane basu fahimci ƙadiya nasu Ahlulbait ba, wanda ake musu mummunar fahimta ta yadda duk abin da aka faɗa akan su sai mutane su ga ana fifitasu ne akan sauran Sahabbai. Shi yasa har yanzu kamar muna marhala ta farko ne na bayani akan su wanene Ahlulbait da matsayin su da kususiyya su. Idan muka koma tarihi zamu ga cewa da Manzon Allah (Saww) da Sayyida Aliyu tushen su ɗaya ne, asalinsu ɗaya ne. Menene asalin Manzon Allah (Saww)? Shine faɗin Allah (T) da yayi a cikin Alkur'ani ce wa, "Asali M

TAKAITACCEN TARIHI, HAIHUWA DA TASOWAR SHAIKH ZAKZAKY (H)

Image
Saura Kwanaki 15 Shaikh Zakzaky Ya Cika Shekaru 70 -Saifullahi M. Kabir TAKAITACCEN TARIHI, HAIHUWA DA TASOWAR SHAIKH ZAKZAKY (H) Ranar Talata 15 ga Sha’aban, 1372 aka haifi Jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), a unguwar Kwarbai da ke birnin Zariya ta jihar Kaduna. Mahaifinsa shine Malam Yaqoub dan Malam Ali dan Sharif Tajuddeen, shi kuma dan wani babban limami da ake kiransa da Liman Husaini. Kakan Shaikh Zakzaky na uku ya kasance daga cikin mutanen Shaikh Usman Danfodiye, wadanda ya tura su garuruwa a matsayin wakilansa, sai ya zama shi Malam Muhammad Tajuddeen Shaikh Danfodiye ya turo shi Lardin Zazzau ne a matsayin mai ba Amir din Zazzau, Malam Musa shawara da taimakonsa wajen tafiyar da harkokin al’umma akan tsarin Musulunci. A wata hira da aka yi da Shaikh Zakzaky dangane da tarihin rayuwarsa a shekarun baya, ya bayyana cewa: “Mahaifina Malamin Alkur’ani ne, haka ma kakana shima Malamin Alkur’ani ne, haka ma uban kaka na. Sai dai shi uban

Cikakken Tarihin Hammad Ibraheem Zakzaky

Image
Cikakken Tarihin Hammad Ibraheem Zakzaky Haihuwarsa An Haifi Sayyid Hammad Ibraheem Zakzaky Ne A Rana mai Kamar ta yau 01 ga Sha'aban 1417 Hirari dai-dai da 10 Ga December 1996 Miladiyya. A Cikin Birnin Kadunan Tarayyar Nijeria. Sunansa Da Laqabin Sa. Sunan sa Sayyid Hammad Ibraheem Anai Masa Laqabi Da Saajid.  Nasabarsa Ta Wajan Uba Nasabarsa  Ta Wajan Mahaifin Sa: Sayyid Hammad, Shine Dan Allamah Ibrahim Zakzaky, na 7, Shi Kuma Dan Malam Yaqoub Shi Kuma Dan Malam Aliy Dan Malam Muhammad Tajuddin Dan Liman Husaini. Shi Liman Husaini Wani Bawan Allah Ne Kuma Babban Malami Da Yake Limanci A Wani Masallaci A Lokacin. Malam Muhammad Tajuddin Yazo Birnin Zariya Ne Daga Sokoto A Cikin Tawagar Amir Na Zariya. Wato Lokacin Da Shaikh Usman Dan Fodiyo (Ra) Ya Na Da Malam Musa A Matsayin Amir Na Lardin Zazzau Sai Ya Hada Shi Da Malam Muhammad Tajuddin A Matsayin Mai Bashi Shawara, Da Kuma Mai Taimaka Masa Wajan Tafi Da Harkokin Jama'a Akan Tsarin Musulunci. Assalin Iyayen Su,

KO KUN KARANTA CEWA; Mace Mutum Ce, Kuma Dai-Dai Ta Ke Da Namiji?...

Image
KO KUN KARANTA CEWA; Mace Mutum Ce, Kuma Dai-Dai Ta Ke Da Namiji?... Wani abu shi ne; Minene dalilin da ya sa aka ce mata su kauda ganinsu daga  maza? Mi yasa kuma aka ce maza su kauda ganinsu daga mata? “QUL LIL MUMINEENA YAGUDDU MIN ABSARIHEEM WA YA'ANFITU FURUJAHUM... WA QUL LIL MUMINATI YAGBIDHNA...” Mi yasa aka fadi wannan?. Na (1) saboda duk lokacin da mutum ya kalli macen da ba tasa ba kuma ba tare da hijabi ba to sai wani juzu’i (bangare) na sha'awarsa ya tafi (cikin sha’awarsa 100 za a kasa a dauki wani bangare a watsar da shi. Idan ya zama shi ne al'adarsa to za a wayi gari ko matarsa ya gani ba ya sha’awarta, ko tazo kusa da shi bai jin komai. Haka nan macen da ta saba ganin maza, su tsura ma maza ido, to ita ma za a wayi gari yau da gobe sha'awarta na tafiya, sha'awarta na tafiya za a wayi gari ko mijinta bata sha’awa. Akwai hikima cikin dokokin Allah, da tsarin Allah.  To ba zamu biyewa ’yan duniya ba masu ganin cewa; ’yancin mata shi ne a s

HOTUNAN TARON YAUMUS SHUHADA'U 1442/2021

Image
Hotunan Taron Yaumus Shuhada'u Na Harkar Musulunci a Najeriya, Wanda Ya gudana Yau Lahadi 23 Ga Rajab, 1442 (07/03/2021) a Garin Suleja.

Gangamin 'Yan maja; Sunji tsoron tunkarar Gaskiya

Image
```Gangamin 'Ƴan Maja.``` Sun Ji Tsoron Tunkarar Gaskiyar Sheikh  Abduljabbar Ne !  -Inji Sheikh Adamu Tsoho Jos.  Maganar 'Ƴan Maja nake yi, zuwa yanzu 'Ƴan Maja sun 'majance' domin sun razana sun san cewa in an zo anyi wannan muƙabala to za a sha kunya ne, daman a cikin kunya suke. Don haka yanzu suna magana cewa wai anje kotu kuma kotun ta bada "Izini" kada ayi wannan muƙabala. To, ko ayi muƙabala ko kada ayi muƙalaba ita fa gaskiya sunan ta gaskiya ce, ba a nasara akan gaskiya. Gaskiya da mai gaskiya ba a taba nasara akan su. Amma ƙaryan mai ƙarya fa ? Kuma an ce Ramin mai ƙarya ƙurarriya ce don haka malaman Maja Ramin su ya ƙure.  Sai ya zama an sa ranar Lahadi gaskiya zata tunkari ƙarya, to kuma daman tun kan a je ko ina mun san wannan mutane ba zasu iya ba. Idan kana maganar shi'a ne kaje ka duba tarihi ba a taba muƙabala  da ɗan shi'a anyi nasara akan sa ba. Domin wanda yayi riko da Alkur'ani da Ahlulbait wallahi ba za a tab

ANYI TARON TUNAWA DA SHAHIDAI A ABUJA 07/03/2021

Image
RANAR SHAHIDAN HARKA ISLAMIYYA Muhd Idris A yau ne aka gudanar da bikin tunawa da shahidan harka Islamiyya da aka saba yi duk shekara a garin Suleja karo na 30. Shugaban Mu'assar ta kasa Sheikh Abdulhamid Bello ne ya kasance babban bako mai jawabi inda ya jaddada ma yan uwa nauyin da ke kansu na sauke hakkin shahidan na harka. Malamin ya ankarar da cewa har kawo yanzu dai abin mamaki ba a sauke shi wannan hakki kamar yadda ya kamata.  Tun kafin haka sai da ya kawo matsayin shahada da kuma shi kansa shahidi a musulunci, da ya dawo ga azzalumai kuma ya ce na da can ma ba su iya hana harka ba bare na yanzu, ya zaiyano yadda azzaluman kasar nan suka rika aukar da waki'a daya bayan daya ana samun shahidai har kawo yanzu. Ya kuma kara kira ga yan uwa wajan kokarin sauke hakkin Jagora a kansu. Farfesa Abdullahi Danladi shi ya gabatar da takaitaccen jawabi tun da fari kan aiyukan ita wannan Mu'assar ya kuma yi godiya ga yan uwa kan kokarinsu gareta. Kamar kowace shekara

Papa Roma Ya Ziyarci Ayatollahi Ali Sistani A Kasar Iraqi.

Image
-Nasir Isa Ali. Shugaban Kirista na duniya, Papa Roma Francis, ya ziyarci babban Malamin Musulunci na kasar Iraqi, Ayatullahil Sayyid Ali Sistani a ofishinsa da ke birnin Najaful Ashraf mai tsarki. Papa Roma ya isar ma sa da sakon Vatican na neman kawo karshen tsattsauran ra'ayin wahabiyanci na SALABIYANCI, da kuma yadda za a zauna da juna lafiya a kasar ta Iraqi. Su dai 'yan wahabiya karkashin ISIS, sun rika yi wa Kiristocin Iraqi da Syria yankan rago tare da babbaka su da ransu har sai  sun mutu tare da yi wa Matansu munanan fyade da kuma koya wa yaransu kanana da 'yan matansu shan wiwi da miyagun kwayoyi duk da sunan Musulunci, domin wai su kore su daga kasar Iraqi.

Sabunta Muzaharorin 'Free Zakzaky' A Nijeriya: Yadda Muzaharar 5 ga Maris 2021 Ta Zo Da Sabon Salo A Da'irar Katsina.

Image
Daga Auwal Isa Musa. Kamar sauraran takwarorinta, Da'irar Katsina ita ma ta bi sahunsu wajen gudanar da jerin gwanon #Freezakzaky a ranar Juma'ar nan 21 ga Rajab, 1442 H (5 ga Maris, 2021), Muzaharar wadda aka gudanar a fadin Kasar baki daya. Muzaharar ta Katsina wadda ta motsa a lokaci guda da misalin karfe 3:00 na rana, ta samu halartar daruruwan 'Yan uwa Musulmi daga sassa daban-daban na Da'irar. Wani sabon salon da Muzaharar ta zo da shi a wannan karon shi ne, yadda aka kalkasa ta zuwa Yankuna  guda Hudu (Zones) na Da'irar, wato Yankin Gabas, Yankin Yamma, Yankin Arewa da Kuma Yankin Kudu, tayadda kowanne Yanki ya gudanar da tashi Muzaharar a lokaci guda da salon da ya dace, aka tashi a inda ya dace, kuma aka tuke ta a inda ya dace. Yankunan masu sunaye kamar haka: Zone 'A', Zone 'B', Zone 'C' da kuma Zone 'D', salon yadda kowannensu ya gudanar da tasa Muzaharar ya bada Natija, domin ta isar da sako ba kadan ba. Yankin Gabas wato